Buhari, Osinbajo, da wasu da dama su biyan harajin jam’iyya – Bincike

0

Shugaba Muhammadu Buhari, Mataimakin sa Yemi Osinbajo, Bola Tinubu da dukkan sauran ‘ya’yan jam’iyyar APC, ba wanda ya biya harajin kudin tallafin jam’iyya na shekarar 2015, kamar yadda rahoton jam’iyyar ya nuna.

Rahoton wanda APC ta fitar, jam’iyyar ta ce a shekarar 2015 ba ta samu ko sisi a hannun mambobin ta ba, wanda hakan ya jefa jama’a cikin tambayar a ina jam’iyyar APC ta bilyoyin kudaden da ta yi kamfen da su a 2015?

Ba a san takamaimen mambobin jam’iyyar APC ko nawa ne adadin su a fadin kasar nan ba.

Amma dai wasu jami’an cikin jam’iyyar sun tabbatar da cewa sun haura miliyan daya.

A duk karshen wata ko kuma karshen shekara, APC na karbar harajin taimakon raya jam’iyya daga mambobin ta.

A cikin 2014, kididdiga ta tabbatar da cewa APC ta tara naira miliyan 23.7.

Sai dai kuma abin mamaki shi ne yadda yadda jam’iyyar ta fito ta ce ba ta tara ko sisi a cikin 2015.

Wannan ya sa an fara tambayar ina ta samu kudin da ta yi kamfen, tunda a cikin 2014 naira milyan 23.7 kacal jam’iyyar ke da shi.

Da yawan masu sharhi, kamar irin su Eze Onyekpere, sun jaddada takaicin cewa jam’iyyar APC ta dogara ne daga samun kudi daga aljihun wasu manyar jigajigan da suka wawura suka boye, irin wadanda jam’iyyar ta yi alkawarin cewa idan ta hau mulki za ta yi yaki da irin su.

“ Hakan ya nuna akwai matsala fa sosai, domin dukkan wadannan masu damfara wa jam’iyya kudade, idan aka ci zabe sai fa ka saka masu da wani abin da ba daidai ba, domin ba fa kudin sadaka ba ne suka baka.”

“Ai duk irin wannan ne ke sa ana karin kudi a kan kudin ka’idar kwangiloli a gwamnati kuma hakan ne ke assasa cin hanci da rashawa.

Idan ba a manta ba dai cikin watan da ya gabata ne jam’iyyar APC da PDP suka fitar da rahoton kudaden da suka kashe a zaben 2015.

Dukkan jam’iyyun biyu dai sun bayyana rahoton cewa sun kashe bilyoyin nairori. Wannan ya sa an fara tambayar shin APC ta samu na ta kudaden tunda a 2014 Naira milyan 23.7 kacal ta ke da shi, yayin da a 2015 kuma ba ta tara ko naira dubu daya ba?

A cikin rahoton da APC ta mika wa INEC, jam’iyyar ta ce a cikin 2015 ta tara naira miliyan 329.4 daga sayar da fam ga ‘yan takara. Sai kuma wata naira miliyan 275 da jam’iyyar ta ce sun fito ne daga jama’a daban daban a matsayin gudummawa ga jam’iyya.

Dukkan jami’an APC har da Sakataren ta Bolaji Abdullahi sun ki yin magana a kan wannan batu.

Abdullahi ya ce wa PREMIUM TIMES ta tuntubi mai binciken kudi na jam’iyya, George Moghalu.

Moghalu ya ce ba zai yi magana ta wayar tarho ba, sai dai a hadu da shi gwa-da-gwa. Har zuwa lokacin da ake rubuta wannan labari bai yarda an hadu da shi ba.

Idan ba a manta ba, ana zargin gwamnatin Muhammadu Buhari da nuna bambanci wajen aiwatar da yaki da cin hanci da rashawa.

Ana ganin gwamnatin ta rufe ido daga binciken wasu jiga-jigan gwamnatin da ake zargi cewa, musamman wadanda ke kan mukamin gwamna a lokacin zaben 2015, cewa sun yi amfani da kudaden jhohin su sun dauki nauyin kamfen din jam’iyyar APC.

A baya-bayan nan ma wani kamfanin buga fasta ya kai APC kara kotu, ya na neman cikon kudin buga fasta sama da naira miliyan 70, da ya ce tun bayan cin zabe jam’iyyar ta ki biyan sa.

Share.

game da Author