Daga mai hankali zuwa kwarkwartacce, shagirigirbau, dukan-shaho ko motsatstse, ba wanda zai ce idan an yi kisa ko kashe-kashe, tilas a samu mai laifi a rikicin ba. Tun daga rikicin addini ko na kabilanci ko fadan Fulani makiyaya da manoma, haka kawai kisa bai dirgowa daga sama, ko ya tsage kasa ya fito ya dauki rayuka ta hanyar yin amfani da makami, ba tare da wani ne ya yi kisan ba.
Haka kuma babu yadda za a iya shawo kan wannan balbalin bala’i sai dole an samu wadannan nau’o’in kwararru da ke cikin al’umma ba su watsar da son rai da kabilanci ko bambanci ko kuma nuna rashin sanin iya aikin da ya wajaba a kan su ba.
GUDUNMUWAR ‘YAN JARIDA
Ba zan ce kafafen yada labarai ba, sai dai kai tsaye na fito na ce ‘yan jarida, domin su dai ne ke watsa bayanan da duk mu ke karantawa ko gani a jaridu da radiyo da gidajen talbijin din da ake kira kafafen yada labarai.
‘Yan jarida sun yi lalacewar da babu ruwan su da irin barnar da kananan kabilu ke yi wa Fulani makiyaya. Idan an kashe Bafulatani a cikin daji ko wani kurmi, an kashe shanun sa, ko an sace, wannan duk ba labari ba ne, saboda su na yi wa Fulani kallon dolaye kuma sun dauke su kamar masu kaskantan daraja a cikin kabilun Najeriya.
Sai ranar da Bafulatani ya kai harin daukar fansa, to a ranar duk wata jarida ko radiyo da talbijin, ba su da wani labari sai na Fulani.
Don an kashe Bafulatani a wurin kiwo shi da ‘ya’yan sa ko kannen sa, an kwashe masa shanu na naira maliyan 10, wannan ba abin bugawa a jarida ba ne, har sai ranar da ya je ya kai hari, ya banka wa bukkar naira dubu 20 wuta, to a ranar shi ne dan ta’adda a fahimtar ‘yan jaridar Najeriya.
Yadda Bafulatani ya ke da matsolanci da mako, wanda kashe kudi don amfanin kan sa ma ji ya keyi kamar tsokar jikin sa ce zai yanka, da wuyar gaske ya fara tsokanar rikici a cikin kabilu sama da miliyan daya, alhali shi da ‘yan uwan sa ba su kai 300 a cikin kabilun ba.
Ai ya san idan ya ja rikici, shi ke da asarar shanun sa da sauran dabbobin sa. Amma a irin wannan rayuwa, duk lokacin da aka matsa musu lambar hare-hare da sace-sace, kuma hukuma da gwamnati ta ki yin wani abu, to su ma fa sun iya fusata, kamar irin yadda wasu kabilu ke fusata su dora wa barayon bokitin roba tayar mota su kone shi.
GWAMNATIN JIHA KO TA TARAYYA
Duk rashin gaskiyar kabilun da ke cikin jiha, to su gwamnatin jihar za ta goyi baya, idan har rikici ya barke tsakanin su da makiyaya Fulani. Idan an kashe Fulani ba za ka ji gwamna ya na magana ba, sai ranar da suka dauki fansa, to a ranar zai fito ya na kakabi da babatu.
Haka ta faru a jihar Taraba, inda gwamna ya bada umarnin a saki ‘yan kabilar jihar wadanda suka kashe daruruwan Fulani a Mambilla, cikin 2017.
JAMI’AN TSARO
Sun kasa aikin su da ya wajaba a kan su na damke duk wanda ya yi kisa su gufanar da shi. Kuma su ake bari da babban nauyin kwantar da tarzoma idan ta barke. Ta kan kai su ga rasa rayukan su kamar yadda ta faru a jihar Nassarawa a shekarun baya, kuma har yau babu abin da gwamnati ta yi a kai. Kuma a kullum hakan na ci gaba da furuwa.
KABILUN TSAKIYAR NAJERIYA
Mu na ganin yadda a kudancin kasar nan ake daukar dukiya da muhimmanci, har ta kai ko faifai ko faranti kai ko gammon daukar kaya barawo ya sata a cikin Legas ko garuruwan Kudu, to taya za su rataya masa su banka masa wuta.
To idan haka wasu kalibun kasar nan suka rike dukiya da daraja, haka shi ma Bafulatani ya dauki dabbobin sa da daraja.
Ka sace shanun mai kiwo, ka kashe masa yara, ka kashe masa shanu saboda kawai saniya daya ta ci maka ganyen rogo ko ganyen dankali na naira dubu uku, kai ma ka san ka tsokano rikici. Idan ma ka na tunanin ba zai rama ba, to ka cuci kan ka da ka dauki doka a hannun ka.
GWAMNATIN TARAYYA
Matsawar saboda siyasa ba a hukunta wadanda ke yin kisa, matsawar idan an kashe Fulani an sace musu dukiya ba a cewa komai, matsawar idan Fulani sun yi ramuwar-gayya ba a hukunta su kamar yadda za a hukunta wadanda suka fara yi musu kisa, to ni dai ban ga ranar warware wannan matsala ba.
Ko an shekara ana jibge jami’an tsaro, ana kai helikwafta, ana kai duk wani makami, ana canja kwamishinan ‘yan sanda, to wannan ba ita ce hikimar ba. Adalci shi ne babbar hikima.
Duk wadannan ba su sa wanda aka fara yi wa barna ta asarar dukiya da rayuka ya manta abin da aka yi masa. Idan wani ya hakura, wani fa ba zai hakura ba, ko ba-dade, ko ba-jima sai ya waiwayo.
Rashin adalcin da ‘yan jarida ke yi shi ma matakin farko ne da zai sa gwamnati ta kara tashi ta fahimci rikicin da idon basira, idan har ta na da basirar sanin wannan basira.
Kuma babu abin da ‘yan jaridar nan ke haddasawa sai cutar da kasar nan baki daya. Amma su a mummunan tunanin su, Fulani suke cutarwa.
Hausawa dai sun ce mai hankali shi ke wanka da ruwa cikin cokali, har ya rage na kuskurar baki.