A wani kara da da wata mata mai suna Monsurat Ogundipe ta shigar Kotu dake Agege dake jihar Legas, ta roki kotu da ta raba auren ta da Mijinta mai suna Sherrif saboda kaurace mata a gado da yayi har na tsawon shekaru 2.
Mansurat ta shaida wa kotu cewa bayan kin kulata da yake yi, ya zama tataccen mashayin giya, domin kullum a buge ya ke dawowa gida.
” Gaba daya yanzu hankalin Sheriff mijina baya muradi na da’ya’ya na. Shi dai ya sha giyar sa ya kuma nemi matan banza a waje ne ya sa a gaba.
Shi ko mijin Mansurat Sheriff bai karyata wannan korafin da Mansurat ta yi a kan sa ba sai dai ya ce yayi haka ne domin ya dawo wa kansa daraja da kima a matsayin sa na mijinta. Yace Mansurat ta raini sannan bata ganin shi da gashi ko kadan.
” A dalilin irin wadannan rashin mutunci ne da Mansurat take gurza mini yasa na fatsama duldular giya kullum. Ni ma kai na na gaji da aure na da Mansurat, ina rokon kotu da ta raba auren kawai kowa ya huta.
A karshe alkalin kotun Ibironke Elabor ya shawarce su da su koma gida su sassanta kan su. Sannan ya daga shari’ar zuwa ranar 26 ga watan Yuli.