Ministan kiwon lafiya na Najeriya Isaac Adewole ya bayyana cewa yara sama da 100,000 dake yankin arewa maso gabashin kasar nan na bukatan ayi musu allurar rigakafi cututtuka.
Ya ce an sami matsala a iya magance matsalar rigakafin ne saboda aiyukkan Boko Haram a yankin wanda ke hana masu yi wa yara allurar iya walwala da ganin yaran ma su kansu.
Adebowale ya ce duk da wannan matsala da aka samu a Najeriya ta sami nasarar kawar da cutar a wasu bangarorin kasar nan amma ya tabbatar da cewa gwamnati za ta zage damtse don ganin wadannan yara sun sami yi allurar rigakafin domin samun sauki a rasa su da ake yi a dalilin haka.