ACPN ta kona magungunanwa’adin amfanin su ya cika ba a yi amfani da su ba

0

Shugaban kungiyar masana magunguna na Najeriya (ACPN) Sunday Ike ya bayyana cewa kungiyar su ta kona magungunan da wa’adin amfanin su ya cika a babban birnin tarayya Abuja.

Ike yace magungunan da suka kona din zai kai ta Naira miliya 452.

Ya ce sun kona wadannan magunguna ne tare da hadin gwiwar hukumomin kula da magunguna na kasan kamar su NAFDAC,NDLEA,PCN da PSN.

“Mun sami wadannan magunguna ne daga hannun wadannan kungiyoyi kuma sun yi haka ne domin yin biyayya ga dokokin aikunsu da kuma don kare kiwon lafiyan mutane.” Inji Ike.

Share.

game da Author