Babbar Mai Shari’a Binta Nyako, ta bada belin sauran ‘yan kungiyar neman kafa kasar Biafra su hudu da ake tuhuma tare da shugaban su Nnamdi Kanu.
Nyako da ke Babbar Kotun Tarayya a Abuja, ta bada belin su a yau Litinin a kan naira miliyan boma kowanen su.
Ana tuhumar Bright Chimezie, Chidiebere Onwudikwe, David Nwawuisdi da Benjamin Madubugwu da laifin hadin-baki su ci amanar kasar su Najeriya.
Da ya ke tuhuma uku ake yi musu, dayan tuhumar kuma ita ce mallakar muggan makamai ba bisa ka’ida ba.
An cafke su ne tun cikin 2016, kuma tun a lokacin suke tsare.
Nyako ta ce ta bayar da su beli ne bisa ga yin nazarin da ta yi ciki har da yin la’akari da tsawon lokacin da suka dade a tsare.
Ta ce ta kuma kara yin la’akari da irin halin rashin lafiyar da wadanda ta bayar da belin suke ciki.