Kungiyar Kwallon Kafa ta Senegal, ta yi nasara a kan ta kasar Poland da ci 2-1 a wasan ta na farko a gasar.
Wannan ne karo na farko da wata kasa daga Afrika ta yi nasara, tun farkon fara wasan a makon da ya gabata.
Dan wasan Poland Thiago Cionek ne ya fara antaya kwallo a ragar su a kokarin sa na hana kwallo shiga raga.
Shigowar M’Baye Niange ke da wuya ya jefa kwallo ta biyu a ragar Poland, a wasan su a Rukunin H da aka kammala ba da dadewa ba a birnin Moscow.
Senegal ta shige gaba tun a minti na 37, lokacin da dan wasan Poland ya ci kan su da kan su.
Kwallon da Poland ta jefa a daidai minti na 86 ya kara wa ‘yan wasan kwarin guiwa, sai dai kuma tuni wuri ya rigaya ya kure musu.
Duk da alkalin wasa ya kara minti biyar, hakan bai sa Poland ta kara jefa kwallo ba.
Wannan wasa ya fitar da Afrika kunya, domin babu wata kasar Afrika da ta yi nasara kafin wannan wasan.
Najeriya da ake ganin za ta yi wani kokari, ta sha kashi a hannun Croatia da ci 2-0.