RASHA 2018: Kasar Masar ce ta farko da aka fidda a gasar

0

Kasar Masar wato Egypt ce kasa ta farko da aka fidda a gasar cin kofin duniya da ake buga wa a kasar Rasha.

Kasar Rasha ta lallasa Egypt da ci 3 da 1.

Shahararren dan wasan kasar wato Mohammed Salah ne ya jefa kwallo daya bayan sun sami bugun daga kai sai gola.

Kasar Urugay ta doke ta da ci 1 mai ban haushi a wasan farko da kasar ta buga.

Yanzu zata kara da kasar Saudi Arabiya ne a wasan karshe na rukunin farko kafin ta tattara nata-ina ta da koma gida.

Rasha ce kasa ta farko da ta tsallaka zuwa zagaye ta biyu bayan ta samu nasara a wasannin ta biyu a jere.

Zata buga wasan ta na karshe da kasar Urugay a makon gobe.

Share.

game da Author