Ministan kiwon lafiya Isaac Adewole ya bayyana cewa akwai yara sama da 100,000 a yankin arewa maso gabashin kasar nan da basu sami yin allurar rigakafin cutar shan inna ba.
Adewole ya fadi haka ne a taron samun madafa game da bullowar cutar a yankin kasashen Afrika wanda aka yi a Abuja ranar Litini.
Gwamnatocin kasashen Afrika tare da kungiyoyin bada tallafi sun hallarci wannan taro ne domin tattauna hanyoyin shawo kan cutar da kasashen Afrika kamar su Kenya, Equatorial Guinea, Guinea Bissau, Angola, South Sudan, Central Africa republic, Mauritania da Nigeria ke fama da su.
A bayanan da ya yi Adewole ya ce cutar shan inna ta sake bullowa ne a Najeriya musamman a jihar Barno sanadiyyar aiyukkan Boko Haram wanda hakan ya hana ma’aikatan lafiya yi wa yara allurar rigakafin cutar a bangarorin jihar yadda ya kamata.
A karshe shugaban taron Rose Leke ta bayyana cewa koda yake gwamnatin Najeriya na iya kokarin ta don ganin ta kawar da bullowar cutar sai dai kamata ya yi duk sauran bangarorin gwamnatin ta hada hannu da gwamnatin tarayya domin ganin hakan ya yiwu.
” Yin hakan ne kadai hanyar samun tabbacin rabuwa da wannan cutar a kasar.”
Discussion about this post