Kotu ta kwace naira biliyan 9.2 da wasu daloli miliyan 8.3 da aka danganta da Patience Jonathan

0

Babbar Kotun Tarayya da ke Lagos, ta bada umarnin a hana matan tsohon shugaban kasa Patience Jonathan kai hannu kan wasu makudan kudade da suka hada da naira biliyan 9.2 da kuma dalar Amurka miliyan 8.3.

Mai Shari’a Mojisola Olatoregun ce ta bayar da umarnin a cikin wani hukuncin da ta yanke a yau bayan da Hukumar EFCC ta shigar da karar neman kwace kudaden.

Tun a ranar 20 Ga Afrilu ne dai lauyan EFCC Rotimi Oyedepo ya shigar da karar.

Mai gabatar da kara ya ce kudaden su na can ajiye a bankin Skye Bank Plc, Diamond Bank da kuma Stanbic Bank sai kuma First Bank Plc.

Baya ga wannan kuma, mai shari’a ta umarci EFCC da ta buga sanarwa a cikin ko da jaridar kasar nan guda daya ce, daga nan zuwa kwana 14, ta sanar da cewa an kulle asusun, an hana Patience ta dauki ko da ficika daga cikin kudaden.

Ba wannan ne karo na farko da kotu ta taba kwace kudade a hannun uwargidan tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ba.

EFCC ta rika maka Patience kotu ne bisa zargin tara makudan dukiya, alhali kuwa ba ta saye, ba ta sayarwa, ba ta dillanci kuma ita ba ejan ba ce.

Dukkan kudaden da EFCC ke bincikowa, hukumar na da yakini ko kwakkwaran zargin cewa kudin gwamnati Patience ta yi fito da shimfida da su, ta kwanta a kai.

Share.

game da Author