Jihar Bauchi ta gina sabbin asibitoci 323 don kiwon lafiyar mutanen jihar

0

Shugaban hukumar hana yaduwar cututtukan zazzabin cizon sauro, kuturta, tarin fuka da kanjamu na jihar Bauchi (BACATMA) Mansur Dada ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta gina sabbin asibitoci domin kare jarirai daga kamuwa da Kanjamau tun suna cikin uwayen su da suka kai 323 a duk kusurwan jihar.

Dada ya fadi haka ne a lokacin da kwamitin kungiyar ‘Maternal and Newborn Health (BASAM)’ na jihar ta kawo masa ziyara ranar Talata.

Ya ce gwamnati ta yi haka ne domin dakile yaduwar cutar Kanjamu sannan da rage yadda mata da yara kanana ke mutuwa a dalilin kamuwa da cututtuka a jihar.

” A lokacin da wannan gwamnatin ta hau karagar mulki a jihar Bauchi asbitocin kula da masu Kanjamu 120 kawai. Wanda a dalilin haka gwamnati ta kara yawan asibitocin domin mata da yara kanana da sauran mutanen dake dauke da cutar a jihar.”

“Mun kuma horas da ma’aikatan kiwon lafiya 700 tare da samar musu isassun magunguna domin kula da wadanda ke dauke da cutar.”

Bayan haka shugaban kungiyar ‘Maternal and Newborn Health (BASAM)’ Isa Ladan ya yi kira ga kwamitin da su tabbatar sun sami adadin yawan mata masu ciki dake dauke da cutar kanjamau a jihar.

Sannan su kuma tabbatar dukkan su na samun magani da kular da suke bukata. Sannan a raba wa mutane musamman mata gidajen sauro kyauta domin kare su daga cizon sauro.

Share.

game da Author