An sa ranar sake zaben fidda-gwanin jam’iyyar APC a Ekiti

0

Jam’iyyar APC ta sake sa ranaar sake zaben fidda gwanin dan takarar zaben gwamna a jihar Ekiti.

Za a sake zaben ne a ranar 11 Ga Mayu, 2018.

Sakataren Yada Labaran Jam’iyyar, Bolaji Abdullahi ne ya sanar da haka a hedikwatar jam’iyyar yau Talata a Abuja.

Sake zaben ya biyo bayan hargitsin da ya auku a wurin zaben fidda gwanin a ranar Asabar da ta gabata. Daga bisani kuma ‘yan takara 27 suka nuna rashin yadda, suka ce tilas sai dai a sake zaben.

Idan ba a manta ba tun bayan zaben da akayi a amkaon da ya gabata, tsohon Gwamnan Jihar Ekiti Shegun Oni, Mashawarcin Shugaba Muhammadu Buhari da wasu jiga-jigan jam’iyyar APC 25 na jihar Ekiti sun nemi a rushe duk wani aikin zaben da Kwamitin Gwamnan Jihar Nasarawa Tanko Al-Makura ya gudanar a zaben fidda-gwani na ‘yan takarar gwamnan jihar.

A cikin watan Yuli mai kamawa ne dai INEC za ta gudanar da zaben gwamna a jihar ta Ekiti

Baya ga wannan, sun kuma yi kira da a soke dukkan kuri’un da kwamitin ya tattara ya ce su ne aka kada a wurin zabukan, wanda ya karke da hatsaniya a fadin jihar.

Sun cimma yarjejeniyar nuna wannan korafi na su bayan da suka tashi daga wani taron gaggawa da suka gudanar a jiya Lahadi, a Ado Ekiti.

Wadanda suka ce ba su yarda da zabukan fidda-gwanin ba, sun hada da tsohon gwamna Segun Oni, Mashawarcin Buhari a kan harkokin siyasa, Babafemi Ujudu, tsohon Sanata Ayo Arise da Gbenga Aluko, Mojisola Yahaya, Bimbo Daramola da sauran su da dama.

Sai da Ministan Karafa da Ma’adinai, Fayemi, bai je wurin taron ba. Dama kuma gungun masu korafin sun yi zargi ne cewa an kwamitin Al-Makura ya tafka cuwa-cuwar kagaggen sakamakon zabe ne don a biya wa Fayemi din bukatar sa ta tsayawa takarar gwamna.

Fayemi, wanda shi ne gwamnan da Fayose ya kayar, a yanzu shi ne a sahun gaban sake neman kujerar, amma a wannan karo, a karkashin jam’iyyar APC.

Akwai da dama masu neman takarar da suka hada Oni da Ujudu da wasu da dama.

Fayemi ya tsaya kai da fata cewa ya na kan gaba wajen kirga kuri’a, don haka sakamakon sauran kananan hukumomi hudu tilas ya tsaya yadda ya ke.

Share.

game da Author