Buhari ya tafi Daura domin taron ‘yan APC na unguwar su

0

Kwana daya bayan dawowa daga Amurka inda ya yi ganawar sa ta farko da Shugaba Donald Trump, Shugaba Muhammadu Buhari ya sake tafiya zuwa Daura, inda zai halarci taron shugabannin APC na mazabu, a mazabar sa ta Kofar Baru 3, a garin Daura.

Jam’iyyar APC dai ta sa ranar da za ta gudanar da zaben mazabu a yau Asabar, 5 Ga Mayu, na kananan hukumomi kuma a ranar 12 Ga Mayu, sai kuma na jiha da za a gudanar a ranar 19 Ga Mayu.

Don haka a yau Asabar kenan Shugaba Buhari za su yi zaben shugabannin jam’iyyar APC na mazabar su ta Mazabar Kofar Baru 3 da ke cikin Daura.

Share.

game da Author