El-Rufai ya yi wa Shehu Sani, Sule Hunkuyi, Danjuma Laah luguden tsinuwa

0

Gwamnan jihar Kaduna ya yi wa sanatoci uku dake wakiltar Kaduna a majalisar Dattawa luguden tsinuwa a taron kaddamar da sabuwar na’urar Zabe da Kamfen din jam’iyyar APC da akayi a garin Kaduna ranar Juma’a.

El-Rufai ya yi aman tsinuwa ga sanatocin uku sannan yayi kira ga mutanen jihar Kaduna da su nemi zabirar su su ajiye a gefe, da zaran sun shigo gari duk su kama su suyi musu talliya.

Ko daya yake gwamna El-Rufai ya ce daya ne za ayi wa talliya, dayan gemu za a aske wa.

” Dalilin da yasa ba sa so a bamu bashi saboda basa so idan an fara aikin hanya a garunku a gama, idan an fara gina asibiti ba sa so a gama, Idan an fara makarantu biyar sauran 10 basa so a gama. A yau babu makiyan talakawan mutanen jihar Kaduna kamar Sule Hunkuyi, Shehu Sani da Danjuma Laah, Allah ya tsine musu, Allah ya mayar musu da aniyar su.” Inji El-Rufai.

Sai dai kuma su mambobi masu wakiltar Kaduna a majalisar Wakilai, yabo shuka sha daga gwamnan. El-Rufai ya yabe su sannan ya jinjina musu kan kokarin da sukayi na ganin sun amince da wannan bashi da aka nema.

Suma wakilan majalisar dokoki na jiha sun sha wannan yabo.

Gaggan APC sun halarci Kaduna ranar Juma’a ne domin kaddamar da kamfen din zabukan Kananan hukumomi da za ayi a Jihar a karshen mako mai zuwa.

” Mun kashe kudade masu yawa domin shirya wannan zabe da ganin an yi nasara. Sannan kuma wannan shine karo na farko da za a yi zabe a kasar nan da na’ura irin wannan da za mu yi amfani da shi.

” Wannan na’ura nuni ne cewa lallai muna tare da jama’a sannan kowa ya yi zabe, abin da ya zaba zai gani.

Ya ce jam’iyyar APC a Jihar Kaduna ta yi aiki tukuru don ganin ta shafe bakin cikin da PDP ta dasa a zukatan mutane.

Ya kara da cewa zuwa yanzu haka gwamnatin APC a Jihar na ayyuka sama da 1292 a fadin Jihar wanda dukkan su ana gab da kammala su.

” Gwamnatin Kaduna ta kashe sama da kashi 60 bisa 100 na kasafin kudin Jihar a fannonin inganta Ilimi da ginawa da gyara makarantu, asibitoci,hanyoyi da samar da ruwan sha.

” Mun gyara fasalin yadda ake gudanar da ayyuka a Kananan hukumomin mu yadda yanzu dukkan su na iya biyan albashi ma’aikatan su. Duk da ko mun taras da rubabbun ma’aikatan da ba a Iya biya watanni aru-aru. Yanzu duk ya zama tarihi.

Shugaban jam’iyyar APC, John Oyegun ya yaba wa gwamna El-Rufai sannan ya yi kira ga mutanen jihar da su ci gaba da mara wa jam’iyyar baya domin ci gaba da nadan romon demokradiya da gwamnan ke kwararo wa mutanen jihar.

Tuni har masu adawa da El-Rufai sun makala masa sunan ‘Idi Wanzami, na Tashar Gagawa.’ Ga ma kadan daga cikin baitin wakar Idi wanzami nan:

“Wanzaman kirki kowa ya na mawashin aska,

Idi Wanzami da dutsen nika ya ke wasawa,

Na Tashar Gagawa koko ya samu bulo na siminti.

Askar sa guda hudu kowace aska ga sunan ta,

Daya kura kin-ci-da-gashi,

Daya ladar ta na jikin ta,

Akwai wata wa aka samu?

Sannan ga kare-dangi.

Idi Wanzami,

A garin ya gogan soda,

Jijiyar wuya ta balle,

Da ya dafa gadon baya na,

Allon kafada ya garye.

Idi Wanzami,

Ya na yi kikar-kikar kamar ya na yankan katako.”

Share.

game da Author