Babbar Kotun Jihar Kogi ta umarci ‘yan sanda su maida Sanata Dino Melaye zuwa Babban Asibitin Kasa da ke Abuja, inda za su ci gaba da kula da shi, yayin da a daya bangare kuma likitoci na ci gaba da kulawa da lafiyar sa.
Babban Mai Shari’a na Jihar ne, Nasir Ajanah ya zartas da wannan hukunci, bayan da lauyoyin Dino suka daukaka karar hukunci da wata kotu ta yanke cewa sanatan ya kasance tsare a hannun ‘yan sanda har sai bayan kwanaki 38 da za a ci gaba da shari’a.
Babban Alkalin ya ce a kai Dino asibitin ne ya zuwa litinin ta mako na gaba, inda za a saurari batun yiwuwa ko rashin yiwuwar bayar da belin sa.
Sau biyar kenan ana jekala-jekala da Sanata Dino Melaye a kan gadon daukar marasa lafiya, tun bayan dirowar da ya yi daga cikin motar ‘yan sanda ya ji ciwo.
A duk ranar da aka dora shi kan gadon daukar marasa lafiya, to ana dora shi sau biyu, a sauke shi kuma sau biyu.
Na farko shi ne an dauke shi ranga-ranga zuwa asibirin Nzimaye na Abuja, daga can kuma ‘yan sanda suka tattage su ka dora kan gado tare da garkama masa ankwa, suka maida shi Asibitin Kasa da ke Abuja. Dauka ta uku kuma ita ce wadda suka ciccibe shi zuwa Lokoja.
A Lokoja ma kafin su karasa da shi kotu, sai da suka yada zango da shi ofishin SARS da ke jihar Kogi, aka bada rahoton gabatar da shi, kamar yadda aka bada cigiyar kamo shi a baya.
Daga ofishin SARS aka gaggauta tallabar sa zuwa Kotun Majistare ta Lokoja. Jiya Juma’a kuma an garzaya Babbar Kotun Lokoja, inda ta umarci a sake ciccibar sa zuwa asibitin Abuja.
Discussion about this post