A bisa dukkan alamu tukunyar siyasa ta fara zababbaka, ganin yadda Shugaba Muhammadu Buhari ya fito da kan sa ya hori jiga-jigan jam’iyyar APC na Yankin Kudu-maso-Yamma cewa su tabbatar APC ce ta yi nasara a zaben gwamnan jihar Ekiti da za a gudanar cikin watan Juli mai kamawa.
Ya yi musu gargadin ne a jiya Labara yayin wata walimar cin abincin da ya shirya wa jiga-jigan jam’iyyar APC na yankin, a Gidan Gwamnati, Abuja.
Ya hore su da su yi iyar karfin su domin su tabbatar cewa dan takarar APC, Kayode Fayemi ne ya yi nasara a zaben.
Ya kara da cewa dukkan mambobin jam’iyyar APC su tabbatar da cewa ba a sauya wa jama’a wanda su ke so, ta hanyar da ba ta dace ba.
“Na san al’ummar jihar Ekiti farin sani, kuma na san su ba su yarda a bude musu ido, masu gaskiya, kuma mutane ne nagartattu.
“Amma abin takaici, duk yanzu al’ummar jihar sun rasa wannan martaba ta su. Tilas mu tashi tsaye mu dawo da martabar jihar Ekiti a matsayin da aka san ta da shi a kasar nan.
“Ganin mun tunkari zaben 2019, akwai matukar bukatar shigo da jihar Ekiti cikin jihohin tafiyar canji. Kuma zaben jihar da za a yi nan da wata daya, shi ne zakaran-gwajin-dafi.
Bayan kammala taron, Bisi Akande ya tattauna da manema labarai, inda ya ce musu sun yi wa Buhari alkawarin cewa sai sun kai masa jihar Ekiti.