Irin abincin da ake ci a Najeriya na yi wa lafiyar mutanen ta lahani

0

Wani likitan zuciya a asibitin Wuse, Abuja, Kunle Iyande ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su rage cin maiko a abincin su sosai kamar su (man gyada da manja) don guje wa kamuwa da ciwon zuciya.

Ya bayyana haka ne da yake ganawa da PREMIUM TIMES ranar Laraba a Abuja.

Iyanda ya yi kira da a rage cin abinci da ke dauke da ‘Carbohydrates’ kamar su doya, masara, rogo, da sauran su domin suma za su iya sa mutum ya kamu da cutar shanyewar bangaren jiki da ciwon zuciya.

” A mafi yawan lokutta na kan gamu da masu fama da ciwon zuciya sannan su ce mun sun rasa abun da za su ci dommin guje wa tada a jikin su saboda sabo da irin abincin da muka ci.

Ya hori jama’a da su kula da abincin da suke ci sannan su rika canza abinci akai-akai domin samun lafiya da gujewa cutuka.

Share.

game da Author