TASHIN FARASHIN DANYEN MAI: Kalubale ga gwamnatin Buhari

0

A karon farko an samu tashin gwauron zabon farashin danyen man fetur zuwa dalar Amurka 80 kowace ganga daya, wanda rabon da ya kai wannan farashi tun cikin 2014, kafin saukar gwamnatin Goodluck Jonathan.

Hauhawar farashin ya faru ne saboda tsoron da ake ji cewa takunkumin da watakila Amurka ke niyyar kakaba wa kasar Iran, zai haifar da karancin danyen man fetur a kasuwannin duniya.

Iran dai ita ce kasa ta uku a karfin yawan hako danyen mai a duniya.

Wani dalilin kuwa shi ne raguwar samun danyen mai daga kasar Venezuela, wadda ita ma ta na a sahun gaba wajen hako danyen mai a duniya.

A Najeriya Shugaba Muhammadu Buhari ya sha sukar gwamnatin da ya gada ta Goodluck Jonathan cewa ta samu kudade a lokacin farashin danyen man fetur bai karye ba, amma ba ta yi komai da kudaden ba.

Sai dai kuma duk da zargin wawurar dukiya da ake yi wa gwamnatin Jonathan, makusantan sa da makusantan wasu gwamnoni na sa, sun hakkake da cewa gwamnatin ta sa da gwamnoni sun yi kokari.

Jonathan, inji su, a cikin kankanin lokaci ya gina jami’o’i 13 na tarayya a fadin kasar nan, haka su ma gwamnonin gwamnatin da dama a Arewa sun gina jam’o’i da sauran ababen da suka tafi suka bari, wannan gwamnati na amfana da shi.

Wadannan jami’o’I da gwamnatin tarayya da na jihohi suka kafa kafin hawan mulkin Buhari, sun taimaka kwarai wajen samar wa matasa damar karatu. Domin da babu su, milyoyin matasa ba za su samu gurabun shiga jami’a a kasar nan ba.

An zargi gwamnatin Jonathan wajen kashe kudade ga aikin fadada manyan titunan shiga Abuja daga Zuba, sai kuma na shiga Abuja da Keffi da kuma na shiga birnin daga Gwagwalada.

Sai dai kuma irin wadannan ayyukan su na nan a na cin moriyar su, musamman wajen saukake wa milyoyin jama’a saukinn shiga da fita Abuja cikin kankanin lokaci.

Ganin cewa yanzu farashin danyen man fetur ya hau sama sosai, a Najeriya za a kara samun kudaden shiga, yadda kason da gwamnatin tarayya ke bai wa kan ta, da wanda ta ke bai wa jihohi da kuma kananan hukumomi duk zai karu.

Wannan ya sa da dama sun fara tambayar junan su shin ko akwai kuma wani dalili da zai sa gwamnatin tarayya ta ci gaba da shirin da a baya ta dauko na ramto makudan kudade domin ta yi aiki da su.

Har ila yau kuma, tunda kason da ake ba jihohi zai ci gaba da karuwa, shin ko akwai wani dalilin da zai sa jihohi za su ci gaba da fita kasashen waje farautar ciwo basussukan da har su sauka daga mulki ba za su ma fara biyan ko kwandala ba?

Sannan kuma wannan karin kudin fetur, kalubale nec ga gwamnatin Buhari domin ta sake zage damtse ta yi wa ‘yan Najeriya ayyukan da ta yi musu alkawari, wadanda da yawa daga cikin su ko tayar da zance su ma ba a yi, ko kuma ba a son a ji wani ya yi.

Matsalar farashin danyen main a daga cikin jinkirin da Majalisar Dattawa ba ta amince da kasafin kudi da wuri ba, har sai jiya Laraba.

Shugaba Buhari yayi kasafin 2018 a kan kirdado da hasashen farashin danyenn mai kan dala 45 kowace gangar danayen mai. Tashin da yayi ya sa Majalisar Tarayya ta maida kirdadon gejin kasafin a kan dala 51 a kowace gangar danyen mai.

Fatan ‘yan Najeriya idan wannan farashin danyen mai yadore, su ga ana gudanar musu da manyan ayyuka wadanda ko bayan babu gwamnatin APC, za a rika cin moriyar su kuma ana tunawa da wanda ya yi aikin.

Share.

game da Author