Wasu Daga Cikin Hakkokan Annabi (SAW) Akan Al’ummarsa, Daga Imam Murtadha Gusau

0

Bismillahir Rahmanir Rahim

Assalamu Alaikum

Ya ku ‘yan uwana masu daraja! Ya ibadah? Ina rokon Allah ya karbi ibaadun mu, yasa muna cikin wadanda ake ‘yantawa a cikin wannan wata mai albarka na Ramadana, amin.

Ya ku bayin Allah! Mu sani, Annabi (SAW) yana da hakkoki akan ko wane Musulmi da ba zamu zama cikakkun Musulmi ba sai mun bashi wadannan hakkoki nasa. Daga cikin su akwai hakkoka kamar haka:

1. Dole ne mu gaskata shi kuma mu gaskata dukkanin abinda yazo dashi, kuma mu gaskata shi a cikin dukkanin abinda ya bada labari.

2. Dole ne muyi masa Da’a, muyi masa biyayya a cikin dukkanin umurninsa.

3. Dole ne mu nisanta kawunan mu daga dukkanin abinda yayi hani daga gare shi.

4. Kar ka yarda kayi ibada ko ka bauta wa Allah sai yadda ya koyar ko ya shar’anta.

5. Dole ne ka kai hukuncin ka zuwa gare shi, kuma dole ne ka yarda da hukuncin Annabi (SAW).

6. Dole ne ka girmama Annabi (SAW) ka kuma girmama Sunnar sa.

7. Dole ne ka kwadaitawa kan ka bin Sunnar Annabi (SAW) da yin aiki da ita.

8. Dole ne yin kira zuwa ga Addinin sa (wato Musulunci), da taimakawa masu kira zuwa ga Addinin sa da bin Sunnar sa.

9. Dole ne yin ladabi da biyayya ga Addinin sa.

10. Dole ne ka so Annabi (SAW) fiye da ‘ya’yan ka, da dukiyar ka, da matan ka, da iyayen ka, da malaman ka, da shehunnan ka, da shugabannin ka, kai da dukkanin mutanen duniya baki daya.

11. Dole ne ka girmama Annabi (SAW), ka girmama Sahabban sa, ka girmama iyalin gidan sa, da sauran dangin sa.

12. Dole ne kayi koyi da Dabi’u da halayen sa.

13. Dole ne ka yawaita yi masa salati da Addu’a, musamman ma ranar juma’ah da daren juma’ah.

14. Dole ne ka girmama Sahabban Annabi (SAW), kayi masu addu’a da nema musu gafara a wajen Allah.

15. Dole ne ka girmama Matansa da sauran iyalan sa da dangin sa.

16. Dole ne ka kyautata ladabi ga Annabi (SAW) a lokacin da yake raye da kuma bayan mutuwar sa.

17. Dole ne a yada Sunnar sa da taimakon ta da yin kokarin yaki da bidi’o’i a cikin addini.

18. Dole ne ka yada alkhairi da zaman lafiya da ya kawo wa duniya, kuma ka kyamaci fitina da tashin hankali.

19. Dole ne kayi amfani da dukkanin abin da Allah ya hore maka na mulki, ilimi, dukiya, karfi, lokaci, matsayi da hanya ka ciyar da Addinin sa da Sunnar sa gaba.

20. Dole ne ka zama mai hakuri, ka zama mai juriya akan dukkanin abin da zai same ka mara dadi wurin yada Addinin sa da Sunnar sa.

Ya Allah ka sanya mu cikin ceton Annabi (SAW), amin.

Wassalamu Alaikum,

Barka da shan ruwa.

Dan uwan ku: Imam Murtadha Muhammad Gusau, daga Okene, Jahar Kogi, Nigeria. +2348038289761.

Share.

game da Author