KASHE-KASHE: Kiristocin Najeriya sun yi zanga-zangan a Abuja

0

Kungiyoyin kiristoci mabiya darikar Katolika sun gudanar da zanga-zangar lumana domin nuna rashin jin dadin su da jimamin yadda kashe-kashe ya zama ruwan dare a kasar nan.

Cocin darikar Katolika wace ta jagoranci masu zanga-zangar ta bayyana cewa ta yi haka ne domin kira ga gwamnati da ta gaggauta daukan mataki kan wannan matsala da ya addabi mutanen Najeriya.
Musamman kiristocin da aka kashe a jihar Benuwai.

Shugaban cocin darikar Angilika Nickolas Okoh ya bayyana cewa wannan kashe-kashe bai tsaya ga mabiya kiristanci ba, har da Musulmai ma wanda dalilin haka ya ke kira ga gwamnati ta mai da hankali wajen samra wa mutane da tsaro a duk inda suke.

” Kafin wannan gwamnatin ta hau karagar mulki a kasar nan ta yi mana alkawarin cewa za ta kare rayukan ‘yan Najeriya amma sai gashi yau an wayi gari wasu da ake zargin makiyaya na ta kisar mutane a kasar nan.

A karshe wanda ya wakilci shugaban kungiyar kiristocin Najeriya (CAN) Sanson Ayokunle yace ” Idan shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gaza wurin kare rayukan mutanen kasar nan ya hakura kawai ya sauka daga mulkin a ba wanda zai iya.”

Kiritocin Najeriya sun fadi cewa za su gudanar da irin wannan tattakin a duk fadin kasar nan domin gwamnati ta gaggauta kawo karshen wannan ibtila’i da kasa ke fama da shi.

Share.

game da Author