Titin Birnin Gwari – Funtua, Maboyan masu garkuwa da ‘yan fashi

0

Bayan sace matan aure uku da wasu masu garkuwa da mutane suka yi a kauyen Birnin Gwari, masu garkuwa sun sace wasu mutane shida bayan haka a garin.

Mahara sun kai hari wani kauyen Birnin Gwari inda suka sace wasu mutane shida. Maharan sun shigo wannan kauye ne da dare da misalin karfe 9.

Bayan haka shugaban kungiyar direbobin motocin haya (NURTW) Danladi Duniya da ke safara a wannan hanya ya koka kan yadda hanyar ta zamo bita da alwalanka.

Ya ce gaba daya yanzu babu sun daina bin wannan hanya, wato Birnin Gwari zuwa Funtuwa zuwa Katsina.

” Wannan hanya ya zama bakin damisa, in banda garkuwa da akeyi da mutanen mu da fasinjoji, sannan fashi ko ya zamo ruwan dare a hanyar. Yanzu kam bamu bin wannan hanya kwata-kwata.

Wani direba da ya ba da bayanin yadda suka yi arangama da su ya ce abin kamar shirin fim.

” Da suka bude mana wuta sai motar ta nemi ta kwace mun sai muka nufi daji. Da motar ta tsaya sai na kula cewa fasinja daya ya mutu nan take.”

” Da masu garkuwa suka iso wurin mu sai suka tattaramu suka nufi daji da mu. Da yake dare ne sai na sulale na gudu na bar sauran wadannan mutane.”

Wani bayani da muka samu kuma ya nuna cewa gaba daya wannan yanki ba a zaman lafiya a wurin. Kusan duk mazauna kauyukan wannan daji, sun san masu aikata wannan aiki domin babu wani bako cikin su.

Shi ko kakain rundunar ‘Yan sandan jihar Kaduna Mukhtar Aliyu, cewa yayi a gaskiya basu da cikakken bayani kan abubuwan da ake cewa na faruwa a wannan titi amma lallai kuwa akwai ayyukan ta’addanci da akan samu a wannan hanya.

Share.

game da Author