An rufe shagunan siyar da magani 400 a jihar Adamawa

0

Kungiyar masana magunguna ta Najeriya reshen jihar Adamawa (PCN) ta sanar cewa ta rufe manya da kananan shagunan siyar da magani 400 a jihar.

Jami’ar hukumar Anthonia Aruya wacce ta sanar da hakan wa manema labarai ta bayyana cewa sun yi haka ne domin bankado shagunan siyar da magungunan da ke karya dokar kungiyar sannan da kawar da wasu ayyukan bata gari da suke yi ta hanyar siyar da jabun magunguna.

” Cikin laifukan da muka kama wadannan shagunan sun aikata sun hada da rashin tsaftace muhallin da shagunan suke, siyar da maganin da aka hana siyar wa a kasuwannin kasar nan, rashin lasisi da sauran su.

” A takaice dai mun rufe shagunan siyar da magunguna 400 sannan mun bar wasu 10 domin sun cika sharuddan kungiyar.”

A karshe Aruya ta bayyana cewa sun fara farautar irin wadannan shaguna ne domin kawar da masu gurbata na gari daga cikin su da kuma wadanda ke siyar da jabun magani a jihar.

Share.

game da Author