Gidauniya ta yi wa mutanen Abuja gwajin cutar koda kyauta

0

Gidauniyyar ‘Omotayo Kidney Care’ ta yi wa mazauna gundumar Aleyita dake hanyar zuwa tashar jiragen sama a Abuja gwajin cutar Koda kyauta.

Shugaban kungiyar Omotayo Akinremi ta bayyana cewa gidauniyar ta yi haka ne domin wayar wa mutane kan game da cutar.

” Bincike ya nuna cewa kashi 15 bisa 100 na mutane Najeriya na fama da wannan cuta gashi kuma maganin wannan cutar na da dan kara tsada.

Akinremi ta bayyana wasu hanyoyi da za a iya bi don kauce wa kamuwa da cutar.

” Hanyoyin guje wa kamuwa da wannan cuta da muka bayyana sun hada da yawan shan ruwa, gujewa shan maganin ciwon jiki da shan wasu magunguna ba tare da izinin likita ba da sauran su.”

Share.

game da Author