Masallata sun dakile harin bakin wake a Gashua

0

Wata mata dauke da bam ta gamu da fushin mutanen garin Gashua, jihar Yobe in da masallata suka kama ta a daidai tana kokarin tada bam din dake daure a kugun ta bayan ta kutsa cikin masallaci tare da mutane.

Darektan hulda da jama’a na rundunar ‘Operation Lafiya Dole’ Onyema Nwachukwu, ya jinjina wa masallatan inda ya kara da cewa bayan sun kama matan, sun mika ta ga jami’an tsaro.

Share.

game da Author