Yadda zaben shugabannin jihohi ya kwance daurin tsintsiyar APC

0

A bisa dukkan alamu daga wannan wata har zuwa cikin watan Fabrairu da za a gudanar da zaben 2019, watanni goma masu zuwa kenan, jam’iyyar APC za ta kasance cikin rikici da rabuwar kawunan ‘ya’yan jam’iyyar.

Hakan kuwa ya biyo bayan yadda zabukan shugabannin jam’iyyar ya gudana afadin kasar nan, jiya Asabar.

Ko kafin zaben na shugabannin jihohi, wanda aka gudanar na shugabannin mazabu a farkon wannan wata ma ya zo da rikice-rikice da rigingimu, har ma da kashe-kashe da kone-kone.

Zaben da aka gudanar na shugabannin jam’iyyar APC a jiya Asabar ya farke kullin tsintsiyar jam’iyyar APC, ta yadda a jihohi da dama bangarori sun kama gaban su.

JIHAR NEJA: Ba a wanye lami lafiya a zaben da aka gudanar na shugabannin jiha ba saboda wakilai daga Kananan Hukumomin Lapai, Agai, Mashegu,Tafa, Kontagora, Gbako da wasu kananan hukumonin sun ce ba son ran su aka ce Liman Muhammadu ne Sakataren Jam’iyya ba.

Sannan kuma sun ce ra’ayin su daya a kan fitar da suna Isa Wakili a matsayin Sakataren Yada Labarai, domin ba a bari an yi zabe ba.

Wannan harankazama ta raba wakilan da suka so zabe gida biyu, kuma a bisa dukkan alamu za su koma gida cike da haushin shugabancin Imam Mohammed na jam’iyyar, duk kuwa da hakurin da ya rika ba su cewa a daure a hada kai.

JIHAR ABIA: Jam’iyyar APC ta wargaje gida biyu a jihar Abia, har ta kai magoya bayan Donatus Nwamkpa sun gudanar da na su zaben daban, su ma magoya bayan Ikechi Emenike sun yi na su daban, duk a cikin garin Umuahia, babban birnin jihar.

JIHAR KOGI: Jihar Kogi dama kullum a cikin rikicin siyasa su ke kwana kuma su ke yini. Magoya bayan Gwamna Yahaya Bello na su taron suka yi daban a babban fiin wasa na Lokoja. Su kuma magoya bayan bangaren Audu da Feleke suka taru a firamare ta St. Peters da ke Felele su ka gudanar da na su taron inda suka fitar da shugabannin su na jihohi.

JIHAR LEGAS: A jihar Lagos ma APC ta dare gida biyu. Bangaren Bola Tinubu sun gudanar da na su zaben shugabanni daban. Su ma magoya bayan Fouad Obi, wanda ya raba hanya da Tinubu, sun taru sun yi na su zaben shugabannin daban.

JIHAR ONDO: A nan ne ma aka fi kaurewa da rincimi sosai. Idan ba a manta ba, a cikin jihar Ondo ne za a fitar da shugabanjam’iyyar APC na kasa baki daya.

Alamomi kuma na nuni da cewa Adams Oshimhole ne za a zaba, ba John Oyegun da zai sauka ya sake tsayawa takara ba.

A wanann zabe na shugabannin jiha, an samu barkewar rikici har ‘yann jarida da dama da kuma manyann jiga-jigann jam’iyya su ka ji raunuka.

AKWA-IBOM: A jihar Akwa-Ibom dai an yi zaben shugabanni, sai kuma tabbas tsugune ba ta kare ba, domin an guji mage an koma an sayi biri da tsada.

Abin da ya faru a jihar shi ne yadda aka zabi wadanda ba su cancanta tsayawa takara ba, kamar yadda akasari aka yi zargi. Wannan taka-haye da yawanci ke gani an yi a cikinn jam’iyyar, ya kawo rabuwar kawuna tsakanin jiga-jigai da magoya bayan jam’iyyar APC a jihar.

Sai dai kuma jihohi kamar Anambra da Ebonyi, ba a samu ja-in-ja ba a ga zaben shugaban jam’iyyar a wadannan jihohi, domin sasantawa aka yi a ka bar wa mutum daya a kowace jihar.

A jihar Katsina kuwa shugaban jam’iyyar da kai, Shittu M. Shittu shi ne dai ya sake zama shugaban ta ba ta canja zani ba.

Haka a jihar Borno, dukkan ‘yan takarar da ke biyayya ga gwamna Shettima, su ne suka samu nasarar lashe zabe.

Akasarin zabukan da aka gudanar sun nuna abubuwa biyu. Na farko rabuwar kawuna a cikin APC. Na biyu kuma za a sha jekala-jekalar zirga-zirgar zuwa kotu.

JIHAR KWARA: A jihar Kwara ma ba ta canza zani ba domin kuwa shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki da mabiyan sa sun gudanar da nasu zaben ne a wuri da bam, shi kuma ministan yada labarai Lai Mohammed da makarraban sa sun yi nasu zaben da wani wurin ne. Kakakin Jam’iyyar APC, Gwamnan jihar Abdulfath Ahmed da wasu jiga-jigan jam’iyyar duk sun bi Saraki ne.

JIHAR KEBBI: A jihar Kebbi kuwa babu wanda ya zo yin zaben ne. Jami’an zabe sun isa wuraren zaben amma babu ko mutum daya da suka gani a wannai wuri na zabe.

A jihar Taraba ma, ba a kaya da dadi ba. An samu rarrabuwar kai tsakanin magoya bayan ministan mata Aisha Ismail da wasu ‘yan jam’iyyar da basa ga maciji da ita.

Shima Rochas Okorocha na jihar Imo bai sha da dadi ba domin kuwa ba yadda yake so aka yi ba. Gaba daya ‘ya’yan jam’iyyar sun yi watsi da shine inda suka zabe shugabannin su ba tare da ya iya yin komai a kai ba. Ya fito daga baya yana ta kumbar baki cewa kotu ta dakatar da zaben saboda haka ba zai amin ce da wannan zabe ba.

Share.

game da Author