Kungiyar likitoci na zargin ma’aikatan jinya (JOHESU) da yi wa aikin su zagon kasa

0

A yau Juma’a ne kungiyar likitocin Najeriya reshen jihar Filato (NMA) ta zargi ma’aikatan jinya dake jihar (JOHESU) da kawo musu rudani a ayyukan su.

Shugaban kungiyar Dajel Bulus ya sanar da haka a Jos wa manema labarai inda ya bayyana cewa ma’aikatan jinyan sun garke dakunan da ake ajiyan kayan aiki da kwado domin su hana likitoci aiki ne kawai a asibitoci.

” Ma’aikatan jinya sun garke dakunan da ake ajiyan kayan aikin da mukan bukata domin yin amfani da su wajen duba mutane. Sannan mutanen da ke bukatar a gwada su, ba halin haka.

” Ko da yake ba mu da shaidun da za su nuna su ne suka aikata haka amma mu mun san cewa JOHESU ta yi haka ne domin ta hana mu gudanar da aiyukkan mu ne.

Bulus yayi musu gwalo cewa suna neman a biya musu abin da ba za a taba cikawa ba.

” Yajin aikin nan da kuka shiga bashi da amfani domin bukatun da kuke nema ba irin wadanda za ku iya samu bane.

Ya kuma yi kira ga ma’aikatan jinyan asibitocin jihohi da kananan hukumomi da suka bi sahun yajin aikin da su janye yajin aikin, su koma.

” Sanin kowa ne cewa gwamna Lalong na iya kokarin sa don ganin gwamnati ta biya ma’aikatan kiwon lafiya albashin su da sauran hakkokin su. A dalilin haka ne muke kira ga ma’aikatan kiwon Lafiya da su janye yajin aiki.Kuma gwamnati ta na muku alkawarin cewa ba za ta bari wani dan kungiya ya tozarta Ku ba.

A yanzu haka gwamnatocin dake jihohin Lagos, Kano, Yobe da Neja sun umurci ma’aikatan jinyar dake jihohin su da su koma bakin aiki domin kula da marasa lafiyan da wasu da yawa dake bukatan kula cikin gaggawa.

Share.

game da Author