Wanda ya tafka magudi a zaben gwamnan Ekiti ya tsokano fitina – PDP

0

Jam’iyyar PDP ta gargadi APC cewa ba za ta taba tsayawa ta zuba idanu jam’iyya mai mulki ta tafka magudi a zaben gwamnan jihar Ekiti ba.

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC, za ta gudanar da zaben gwamnan jihar Ekiti ranar 14 ga Yuli, 2018.

Daga nan sai PDP ta ce matsawar APC ta yi magudi a zaben, to ta tsokano mummunan rikicin da ka iya shafar hadin kan kasar nan.

Shugaban jam’iyyar APC ne, Uche Secondus ya bayyana haka, a lokacin da ya ke kaddamar da yakin neman zaben shugabannin kananan hukumomin jihar Rivers, a jiya Alhamis, a Fatakwal, babban birnin jihar.

Secondus ya ce APC na kulle-kullen yin magudi a wurin zaben.

A nan sai ya yi gargadin cewa duk wani kokarin da APC za ta yi, domin hada baki da jami’an tsaro ta ci zaben, to ta makara, kuma PDP ba za ta amince ba.

Share.

game da Author