Kungiyar JOHESU ta ce ba za ta bi umarni Kotu ba

0

A jiya Alhamis ne Kotu ta umurci kungiyar ma’aikatan jinya(JOHESU) ta janye yajin aikin da take yi wa’adin awa 24 su janye yajin aikin da suke yi.

Kotun ta yanke hukuncin haka ne bayan karar da wata kungiya mai zaman kanta mai suna ‘Incorporated Trustees of Kingdom Human Rights Foundation International’ta shigar kan yajin aikin da kungiyar JOHESU ta shiga.

‘‘Gidan jaridar ‘Daily Trust Newspaper’ ta rawaito cewa kungiyar ta shigar ta wannan kara ne domin a tilasta wa kungiyar JOHESU ta janye yajin aikin da take yi, bayan haka sai su sasanta da gwamnati’’.

Kotun ta kuma umurci ministan kiwon lafiya Isaac Adewole da ministan kwadago Chris Ngige da su nada kwamitin da zai Zauna da duka bangarorin domin shawo kan ma’aikatan.

Share.

game da Author