Za a hukunta duk asibitin da taki karbar mai dauke da raunin harbin bindiga

0

Rundunar ‘yan sandan jihar Legas ta gargadi asibitoci da likitoci a jihar da su daina tambayan rahotan ‘yan sanda kafin su duba wanda aka kawo musu da raunin harbin bindiga.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Chike Oti wanda ya sanar da haka ranar Laraba yace yin wannan gargadi ya zama dole ganin yadda ma’aikatan lafiya ke nuna halin ko-in-kula ga wadanda aka kawo su da raunin harbin bindiga.

Ya ce rundunar ta yi wannan gargadi ne domin wayar wa ma’aikatan kiwon lafiya game da sakacin da suke yi da rayukan mutanen da aka harba a asibiti.

” Za a hukunta duk likita ko asibitin da ta ki karbar wanda aka zo da shi asibiti da raunin harbin bindiga.

Share.

game da Author