Jihar Neja ta samar wa manoma taraktoci 130

0

Gwamnan jihar Neja Abubakar Bello ya bayyana cewa gwamnatin sa ta samar da taraktocin noma 130 domin bunkasa aiyukkan gona a daminan bana a jihar.

Ya fadi haka ne ranar Talata a taron raba wa manoma taraktocin da kayan aiki da ka yi a Minna.

” Gwamnati ta yi haka ne domin agaza wa manoman jihar da kuma samar wa matasa aikin yi a jihar.”

Ya ce sun siyo taraktocin noman 130 akan Naira biliyan 2.2 sannan za a siyar wa manoma a jihar akan ragin kashi 25 bisa 100.

” A yanzu haka gwamnati na kokarin karo taraktoci 100 a wani shiri na musamman na babban bankin kasa wato CBN da wasu hukumomi da kungiyoyi domin agaza wa manoman.

Bello yace gwamnati ta siyo injinan casar shinkafa 50 domin manoma su sami sauki wajen casa da kuma samar da takin zama ni da ya kai to, 15,000 ga manoman mu.

Ya ce bayan gwamnati ta samar da wannan taki za a siyar da kowani buhu kan farashin gwamnati na naira 5,500 a jihar.

Share.

game da Author