Jami’in hukumar ba da agajin gaggawa na jihar Barno (NEMA) Ibrahim Abdulkadir ya bayyana cewa wani dan kunan bakin wake ya kashe jami’an tsaron ‘Civilian JTF’ guda biyar sannan mutane shida sun sami rauni a wani hari da ya kai a kauyen Madarari.
Abdulkadir ya ce wannan abu ya faru ne ranar Talata da karfe 1:30 na rana a kauyen dake karamar hukumar Konduga.
” Dan kunar bakin waken ya tada bam din da ke daure a kugun sa a daidai shingen sojoji.
Kakakin jami’an tsaron ‘Civilian JTF’ Bello Danbatta ya bayyana cewa ya rasa ma’aikatan sa hudu tare da shugaban su a Konduga.
Bayan haka rundunar sojin Najeriya ta bayyana cewa wannan rana ta Talata sun kama wasu ‘yan Boko Haram shida a kauyen Gashigar dake jihar Barno.
Jami’in harka da jama’a na rundunar Texas Chukwu wanda ya sanar da hakan ya ce sun ji wa ‘yan Boko Haram da dama rauni sannan sun kwashi makamansu a arangamar da suka yi da su.