• PREMIUM TIMES |
  • Tallata Hajar ka |
  • Adireshin mu |
  • PTCIJ |
  • Dubawa
Premium Times Hausa
  • Labarai
    • All
    • Duniya
    Ba ayi zabe a Katsina ba, coge aka yi kuma za mu garzaya Kotu – Lado-Danmarke

    Hyacinth Alia na APC ya lashe zaben gwamnan jihar Benuwai

    Umar Bago na APC ya lashe zaben gwamnan Neja

    KURUNKUS: Abba Gida-Gida ya doke ɗan takaran Uban Abba, Gawuna na APC da kuri’u sama da miliyan ɗaya a Zaɓen gwamnan Kano

    ZAƁEN GWAMNAN JIGAWA: Namadin APC ya natsar da Lamidon PDP a Jigawa, ya lallasa shi da kuri’u 618,449

    Thugs-attack-collation

    ZAƁEN GWAMNONI YA ƊAU ZAFI: An kashe shugaban PDP bayan an lakaɗa masa dukan tsiya a rumfar zaɓen sa

    2023: Ya mutan Adamawa, ga Tinubu ga Binani na kawo muku su – Shelar Buhari a Yola

    ADAMAWA TA KWASHI ‘YAN KALLO: Binani ta kamo hanyar tururmusa ƙarti 14 a kokawar ƙwace kujerar gwamna

    ZAƁEN GWAMNAN ANAMBRA: Muhimman Abubuwan Da Suka Faru Daga Ƙarfe 11 Zuwa 12:30 Na Ranar Zaɓe

    INEC ta dage zabe a rumfuna 10 a jihar Legas

    ZAƁEN GWAMNA A KANO: Har ƙarfe 12 na ranar zaɓe ana ta raba wa talakawa taliya da atamfofi

  • Labarai daga Jihohi
  • Wasanni
    TSOHO MAI RAN ƘARFE: Obasanjo ya zura ƙwallaye uku a wasan sada zumuntar tsoffin ɗaliban sakandare

    QATAR 2022: Yadda Croatia, ƙasa mai mutum miliyan 4 ta kori Brazil ƙasa mai mutum miliyan 216

    AMBALIYAR QATAR 2022: Spain ta kori kociya Luis Enrique bayan ta kwashi buhun kunya a hannun Marocco

    QATAR 2023: Yadda Walid, kociyan Morocco ya rikita duniyar ƙwallon ƙafa cikin watanni 4 kacal

    QATAR 2022: Dukkan ƙasashen Afrika 4 da su ka taɓa kai wasan kaiwa ga na kusa da na ƙarshe, su na da tauraro a jikin tutocin su

    Abubuwan al’ajabi dangane da fatattakar da Morocco ta yi wa Spain daga Qatar 2022

    QATAR 2022: Ko ƙasashen Afrika za su fidda nahiyar jin kunya a duniyar ‘yan ƙwallo

    DAGARGAZA ARGENTINA: Ƙasar Saudiyya ta ba da hutun kwana Ɗaya a wataya

    QATAR 2022: 2:1: Saudiyya ta kafa tarihin karya gadara da tutiyar buga wasan Agentina 36 a jere babu rashin nasara

  • Kiwon Lafiya
  • Nishadi
  • Bidiyo da Hotuna
    BIDIYO: Buri da fata na a 2023: Ra’ayoyin jama’a

    BIDIYO: Ƙogon Al’ajabi, ƙogon Waraka, Ƙogon biyan bukata a jihar Enugu

    Mutanen Arewa na da alƙawari da sanin ya kamata, Tinubu za su yi saboda ƙauna da biyayyar da ya nuna wa Buhari – El- Rufai

    BIDIYO: NAJERIYA @62: Ra’ayoyin ‘yan Najeriya game da mulkin Buhari a tsawon shekaru 7 da suka gabata

    Buhari bai san ƴan ta’adda sun fidda bidiyon da suka ce sai sun sace shi da ni ba sai da na ziyarce shi – El-Rufai

    Dalilin da ya sa na raɗa wa wasu fitattun gine-gine, da titunan jihar Kaduna sunayen wasu fittattun ƴan asalin jihar

    HOTUNA: Ɗan Autan marigayi tsohon sarkin Kano Ado Bayero, Mustapha Ado Bayero, ya auri mata biyu ranar Asabar a  Kano

    BIDIYO: An yi wa ɗan takarar mu murɗiya a zaɓen fidda gwani na APC a Legas – Masu zanga-zanga

    KURUNKUS: Malami ya fito takarar gwamnan Kebbi, ya ce jama’ar jihar ne suka tilasta masa ya fito

No Result
View All Result

Kwatagwangwamar shari’a, zanga-zanga da tsare El-Zakzaky

Ashafa MurnaibyAshafa Murnai
May 16, 2018
in Ra'ayi
0
Kwatagwangwamar shari’a, zanga-zanga da tsare El-Zakzaky

Shi'a Free El-Zakzaky

Kwatagwangwamar shari’a, zanga-zanga da tsare El-Zakzaky, Daga Ashafa Murnai

Bayan gurfanar da Shugaban Mabiya Shi’a, Sheikh Ibrahim El-Zakzaky, mabiyan sa sun rasa inda shugaban na su ya ke tsare.

Kokarin da lauyan babban malamin mai suna Maxwell Kiyom ya yi domin a bada belin wanda ya ke karewa ya ci tura, domin Mai Shari’a Gideom Kurada na Babbar Kotun Kaduna, ya ce ba za a tattauna batun beli baki da baki ba, sai dai ya rubuto a takarda.

Ba a dai fara sauraren kara ba a jiya Talata, saboda biyu daga cikin wadanda ake tuhumar ba a gabatar da su a kotun ta Kaduna ba.

A kotun dai dandazon jami’an tsaro sun hana magoya bayan El-Zakzaky da ‘yan jarida shiga ko matsawa kusa da harabar. In banda ma’aikatan kotun, ba a bar kowa ya shiga ba.

A wannan ne karon farko da aka fita da malamin tun bayan tsare shi da jami’an SSS suka yi cikin watan Disamba, 2015.

An gurfanar da shi da matar sa Zeenat ne a kotun Kaduna bisa zargi takwas da suka hada da kisa.

Yayin da a wurin hargitsin da ya yi sanadiyyar sojoji suka kashe mabiya malamin sama da 340, an samu rahoton kisan soja daya.

Yayin da har yau ba a tuhumi ko soja daya da laifin kisan mabiyan Sheikh El-Zakzaky ba, an gurfanar da malamin da matar sa bisa tuhumar su da laifin kisan soja daya da haddasa tashin hankali.

Daya daga cikin mabiyan malamin mai suna Abdulhamid Bello, ya bayyana cewa gwanmatin Najeriya ta guji aikata zalunci, domin shi zalunci kaikayi ne, a kan mashekiya ya ke komawa komai daren dadewa.

Ya ci gaba da cewa El-Zakzaky bai karbi sammacin karar da aka kai shi a Kaduna ba, ya ce sai an sake shi kamar yadda kotuna su ka bayar da umarni tukuna tun da farko.

A daya gefe kuma, mabiyan malamin na nuni da cewa ba su sani ba ko an maida shi Abuja a hannun SSS inda suke a tsare shi da matar sa, ko an tsare su a Kaduna.

Sai dai kuma sun jaddada cewa ko ma ina aka tsare shi, hakan ba zai hana su ci gaba da zanga-zanga a Abuja ba, har sai an sake shi kamar yadda kotu ta bayar da umarni.

KAKA-GIDAN MABIYA EL-ZAKZAKY KUSA DA FADAR SHUGABAN KASA

An shiga rana ta 889 kenan mabiyan sa na fitowa kan titinan Abuja sun a zanga-zangar neman a sakar musu jagora.

A kowace rana mazan su da matan su kan hau titina su na rera wakokin neman a sakar musu jagora da kuma la’antar gwamnatin da suke kira azzalumar gwamnatin da ta shanye musu jinin daruruwan ‘yan uwa.

Su kan yi macin da rawar kwamba tare kuma jerin gwanon yin sassarfa kan titi su na yi wa kwalta kirbin sakwara da kafafun su.

Daga nesa masu wucewa a kan motoci ko masu wucewa nesa da hanya, har ma da unguwannin da ke nesa su na rika jin karar dukann kwalta da suke yi da kafafun su, ‘rididif,rididif,ridif, ridif.

Su na wannan didima da kafafun su cike da izza da nuna rashin kasala, tare da cewa, “Mu ke wahalar da jikin mu, amma wasu ke jin zafin abin da mu ke yi, ba mu ba.”

Ba sau daya ba, ba sau biyu ba kuma sun sha yin artabu da ‘yan sanda, wanda hakan ya yi sanadiyar kashe wasu masu zanga-zanga, ciki har da jagoran mabiyar, wato wakilin Sheikh El-Zakzaky na Sakoto, wanda aka sani da Malam Kasimu da kuma wasu daban.

A jajibirin da SSS suka fice da El-Zakzaky zuwa Kaduna, an yi artabu sosai tsakanin ‘yan sanda da mabiyan malamin a Dandalin Eagle Square da Sakateriyar Gwamnatin Tarayya, a Abuja.

Bayan kura ta lafa ne masu zanga-zanga suka rika shelar cewa sun ci gabala akan jami’an tsaron, domin sun gigice su na harbi, har suka yi kuskure suka harbi wani jami’in su da kan su, sun yi tsammanin mai zanga zanga ne.

An kuma nuno hoton wata wata motar jami’an tsaro da masu zanga-zanga suka yi wa kwatsa-kwatsa, har suka rubuta, “FREEE EL-ZAKZAKY” da jan fenti a kan motar.

Shi’a Free El-Zakzaky

Tun da jijifin safiyar Talata suka rika yada sanarwar cewa sun samu labarin an dauke jagoran na su daga Abuja, da misalin karfe 4 na asubahi, aka nufi da shi Kaduna tare da matar sa, domin a gurfanar da su kotu.

A Kaduna ma a lokacin da ake zaman kotu, har bayan kammala shari’a, mabiyan sun yi zanga-zangar neman a sake shi.

Kamar yadda a Abuja jiya Talata dimbin mabiyan maza da mata sun sake hawan kwalta a Sakateriyar Gwamnatin Tarayya, suka ci gaba da zanga-zangar sai-Baba-ta-gani.

SHAWARWARIN A SAKI EL-ZAKZAKY

Cikin watan Afrilu, jaridar Daily Trust ta yi sharhin da ta bayyana ra’ayin ta cewa ta na bai wa gwamnatin Buhari shawara da a saki El-Zakzaky, domin kauce wa sake mummunan rikici mai kama da na Boko Haram a Najeriya.

Shi ma tsohon jakadan Amurka a Najeriya, John Campbell, ya yi kakkausan gargadi ga gwamnatin Najeriya da ta gagguta sakin malamin domin gudun abin da ka iya biyo baya idan tura ta kai magoya bayan sa bango.

An gurfanar da El-Zakzaky kotu, kwana daya bayan da sojojin Isra’ila suka kashe Falasdinawa sama da 50.

Ganin yadda ‘yan Najeriya ke ta nuna jimamin kisan Falasdinawan, daya daga cikin masu zanga-zangar neman a saki El-Zakzaky a Abuja mai suna Yusuf, ya ce “idan an tuna ai Malam zakzaky ne kan gaban mazahara idan ana maganar makomar Falasdinawa.

“Amma an wayi gari a Najeriya ba a ganin laifin gwamnatin Buhari da ta kashe daruruwan musulmi mabiya mutumin da ya fi kowa nuna damuwa idan an kashe Falasdinawa.

“Don munaficci dan Najeriya zai rika kumfar baki an kashe musulmin wata kasa, wadanda da yawn su ma mabiya Shi’a ne a can. A nan kuma an kashe mu amma su na murna, don mu ‘yan Shi’a ne.’’

TSAKA MAI WUYA

Gwamnatin Muhammadu Buhari na cikin tsaka-mai-wuyar fama da rigingimu tun bayan hawan sa mulki.

Watanni shida bayan hawan sa, rikici ya barke a Zaria tsakanin mabiya Sheikh El-Zakzaky da sojoji tagwatar Hafsan Hafsoshin Sojojin Najeriya a lokacin, Janar Tukur Buratai, inda aka yi mummunan kisa, har suka shiga cikin gidan malamin.

Bayan an kashe mutane a cikin gidan sa, an kuma kashe ‘ya’yan sa hudu. An nakasa masa ido daya kuma na ji masa raunuka.

Matar sa Zeenat kuwa lauyan su ya tabbatar da cewa har yau akwai harsasai a cikin jikin ta.

Kafin zaben 2015 kuwa, a fili ta ke cewa duk da malamin babu ruwan sa da shiga harkar zabe ko siyasa, ya nuna fifikon Buhari a kan Jonathan.

Cikin wata hira da jaridar RARIYA ta yi da El-Zakzaky a farkon 2014, malamin ya yi amanna cewa a dukkan takarar da Buhari ya yi sau uku a baya, da bai yi nasara ba, duk magudi aka yi masa.

Gwamnatin Buhari na fama da matsalar kashe-kashe bakatatan a Arewacinn kasar nan, musamman a jihohin Zamfara, Kaduna, Benue, Nasarawa da Taraba.

Har yanzu Boko Haram sun zame wa gwamnatin Buhari tamkar hakin tofa, domin a kullum kashe su ake yi, kuma ana cewa an gama da su, amma kuma kullum ba su daina kai hare-hare ba.

Duk da cewa mulkin farar hula ake yi, amma sama da rabin jihohin kasar nan duk sojoji ne kan gaba wajen sa-idon kula da tsaro, saboda tashe-tashen hankulan da ake fama da su.

Irin yadda ake girke sojoji a cikin yankunan jihohin kasar nan, bai hana ci gaba da yin garkuwa da mutane ba a yankuna daban-daban.

Sau da dama ‘yan fashi sun daina tare hanya, sun fi karkata ga shiga kananan garuruwa da kauyuka kan su tsaye, saboda matsalar tsaro.

A kullum sai kara girka sansanonin sojoji ake yi a yankunan da tashe-tashen hankula suke ci gaba da kamari.

Duk da kirke sojojin da ke ci gaba da yi, hakan bai kawo alamar karshen kashe-kashen da ake fama da su ba, musamman a Arewacin kasar nan.

Irin yadda ake yawan kama muggan magamai daga hannun mahara a kullum a Arewacin kasar nan, ya nuna cewa akwai matsala kwance a kasa sosai.

A Babban Birnin Tarayya, Abuja kuwa, mabiya Sheikh El-Zakzaky a kullum sai kara tudadowa suke yi, su na yin zaman dirshan na zanga-zangar neman a sakar musu jagora.

Tun a na bin su a guje su na tserewa, yanzu sun kai ga dakewa, ana artabu da su da jami’an tsaro, duk kuwa da ba su dauke da ko da bindiga balle sanda ko gora. Sai dai duwatsu kawai.

A yau sun cika kwanaki 890 cif su na zanga-zanga a Abuja.

Tsakanin inda ake artabu da su da Fadar Shugaban Kasa, bai kai tazarar kilomita daya tal ba.

A zaman yanzu dai Mai Shari’a Kurada na Babbar Kotun Kaduna ya daga kara zuwa 21 Ga Yuni, 2018.

Tags: AbujaBirnin TarayyaEl-RufaiEl-ZakzakyJonathanKadunaLabaraiMaxwell KiyomNajeriyaPolicePremium Times HausaShi'aSojojinTattaki
Previous Post

Ba za ni ba ‘yan Najeriya kunya ba – Buhari

Next Post

‘Dan kunar bakin wake ya kashe mutane biyar a kauyen Konduga

Next Post
Boko Haram

'Dan kunar bakin wake ya kashe mutane biyar a kauyen Konduga

Binciko

No Result
View All Result
Karanta

Ramadan Kareem AD

Sabbin Labarai

  • ƊAN HAKIN DA KA RAINA: Yadda Lawal Dare ya kakkaɓo ‘jiragen yaƙin’ Matawalle, Yari, Shinkafi da Yarima a Zamfara
  • ZAƁEN GWAMNONIN 2023: Gwamnonin da su ka kammala wa’adi da zaɓaɓɓun da za su gaje su
  • ANA WATA GA WATA: APC ta ƙi amincewa da sakamakon zaɓen gwamnan Bauchi, ta ce an ɗibga maguɗi
  • TARABA TA JUYE: Kefas na PDP ya zama zaɓaɓɓen gwamna, NNPP ta yi bazata
  • ZAƁEN GWAMNAN BARNO: Yadda Zulum ya zunduma Jajari na PDP rijiya, ya bi ya danne shi da ƙuri’u 545,000

Abinda masu karatu ke fadi

  • auto verkopen on ZAMFARA: Mahara sun gudu sun bar bindigar harbo jiragen sama a dajin Gumi da Bukkuyum -Inji ‘Yan Sanda
  • Laser-Haarentfernung mit hygienischen Bedingungen und aktuellen Gesundheitsstandards in der Türkei on An yi min murɗiya ne a zaɓen APC, ban yarda ba sai an sake zaɓe – Korafin Bashir Ahmad
  • Call Girls Sehore on Ƙungiya ta yi kira ga gwamnati ta ware kuɗaɗe domin samar da dabarun bada tazarar Iyali
  • buy aged stripe account on Hukumar NBC ta gayyaci mai gabatar da shirin ‘Berekete’, bayan macen da ta kona gashin kan yarinya barkatai, ta sha mari barkatai a hannun sa
  • research and survey on Gwamnan Edo ya bijire wa umarnin kotu, ya ce sai mai shaidar rigakafin korona zai yi sallar jam’i a masallaci

Fanni

Tweets by PTimesHausa
  • All Homepage Blocks
  • Home
  • Home
  • Main Home

© 2023 JNews - Premium WordPress news & magazine theme by Jegtheme.