A daren Laraban nan ne Allah yayi wa fitacciyar jaruman fina-finan Hausa Hauwa Maina rasuwa.
Kamar yadda Jarumi, Ali Nuhu ya tabbatar wa PREMIUM TIMES, ya ce jaruman ta rasu ne yau a Kano.
Hauwa ta rasu a wani asibiti dake garin Kano bayan ta yi fama da ciwo.
Tuni ‘yan uwanta masu shirya fim da jarumai suka dinga lika hotunan ta a shafunan su ta Instagram suna yi mata addu’ar Allah yaji kanta.
Muma A PREMIUM TIMES muna mata fatan Allah ya sa Aljanna ce makomar ta, Amin.