Babu dalilin da zai sa in sake goyon bayan Buhari – Obasanjo

0

Tsohon Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo ya ragargaji ziyarar da Shugaba Muhammadu Buhari ya kai Amurka da cewa shirim-ba-ci ba ce.

Obasanjo ya ce Buhari ya yi rashin amfani da damar da ya samu inda a wurin ne ya kamata ya nuna shi shugaba ne wanda ya san abin da yake yi sosai, amma sai ya kasa gabatar da kudirorin ci gaba guda uku da suka jibinci inganta Najeriya.

Obasanjo ya yi wannan furucin ne a fusace, bayan da ya ke maida martani kan wani rahoto da aka rika yadawa, inda aka ce ya ce ya dawo yanzu kuma ya na goyon bayan shugabancin Buhari a zango na biyu.

Yayin da ya ke karyata rahoton, a jiya Laraba Obasanjo ya yi karin haske a cikin wata takarda da kakakin yada labaran sa Kehinde Adeyemi ya sa wa hannu cewa, ya nisanta kan sa daga masu jinjina wa Buhari cewa yayi abin kwarai a ziyarar sa Amurka.

Tsohon shugaban ya kara da cewa har yanzu ya na nan kan matsayin da ya dauka tun a ranar 23 Ga Janairu, inda ya jaddada cewa Buhari bai cancanci sake tsayawa takara a karo na biyu ba.

Obasanjo ya kuma yi kira da ko da Buhari ya sake tsayawa, to kada a zabe shi.

A cikin rahoton da aka ce Obasanjo ya nuna yabo ga Buhari, an nuna cewa ya yi jawabin ne lokacin da wata kungiyar kwadago ta kai masa ziyara a gida, a ranar ma’aikata.

Kan haka ne Obasanjo ya ce shi a ranar bai karbi wata tawagar kungiyar kwadago daga ko’ina ba.

Daga nan sai ya nuna cewa ai ko kwarkwantaccen mutum ba zai so Buhari ya sake shugabancin Najeriya karo na biyu ba. Ciki kuma ya yi nuni da yadda kashe-kahe ke ta kamari a kasar nan.

Share.

game da Author