HARIN MASALLACI: Za a tsaurara matakan tsaro a jihar Adamawa – Inji Osinbajo

0

A dalilin bama-baman da ya tashi a masallaci da kasuwar ‘yan gwanjo dake garin Mubi, jihar Adamawa ranar Talata, mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya bada umurin a kara tsaurara tsaro a yankin.

Maitaimaka masa kan harkokin yadda labarai Laolu Akande ne ya sanar da haka wa manema labarai ranar Laraba.

Ya ce gwamnatin Najeriya ta yi tir da wannan harin da aka kai masallaci da kasuwar garin na Mubi sannan tana mika sakon jajen ta da ta’aziyya ga gwamnati da mutanen jihar game da wannan mummunar abu da ya faru.

Akande ya kuma kara da cewa gwamnati ta jinjina wa musamman ga likitoci da sauran mutanen da suka agaza wa wadanda suka sami rauni sanadiyyar tashin bama-baman.

‘‘Muna tabbatar muku da cewa jami’an tsaro za su hukunta duk wanda aka kama yana da alaka ko hannu a aikata wannan hari.”

A karshe Yemi Osinbajo ya gana da gwamnan jihar Bindow Jibrilla domin samun bayanai kan abin da ya faru a garin na Mubi sannan ya umurci hukumar bada agaji na gaggawa ta kasa (NEMA) da ta gaggauta kai kayan agaji wuraren da abin yafaru da kuma mutanen da ya shafa.

Share.

game da Author