Da Azahar din Talata ne wani yaro da yayi jigida da bam ya tada ta a daidai ana sallar Azahar a masallacin dake Wuro-Burode kusa da yan Gwajo, Mubi, Jihar Adamawa.
Ko da yake ba a bada cikakken bayani kan yawan mutanen da suka rasu ba, wani mazaunin garin yace da yawa daga cikin masallatan sun rasu.