Ministan Kiwon Lafiya Isaac Adewole ya sanar da hana shigowa da sarrafa maganin ‘Codein’ Najeriya.
Hakan ya biyo bayan illolin da aka gano maganin tari da ke dauke da codein ke yi ne wa lafiyar mutane ne.
Idan ba a manta ba shaye-shayen maganin tari da ke dauke da ‘Codein’ ya zamo ruwan dare a kasar nan musamman a yankin Arewa.
An ce sinadarin da ke cikin ruwan maganin ya na da alaka da hodar iblis da kuma garin hodar a-ji-garau.
Rahotanni sun nuna cewa yawancin masu sha kwayoyi na amfani da shi idan ba su iya sayen kwayoyin buguwa masu dan Karen tsada.
Har yau dai gwamnatin jihar Katsina ba ta yi wata doka da ta haramta sha da safara da sayar da maganin na tari da mura ba.
BBC ta nuna wani bidiyo a karshen makon da ya gabata da ke nuna irin illar da maganin tare da ke dauke da ‘Codein’ ya yi wa wasu matsan Najeriya. Inda tayi tattaki zuwa wani gida da ake ajiye wadanda suka samu tabun hankali a dalilin kamuwa shan irin wadannan kwayoyi.
Minista Adewole ya ce daga yanzu ba za a lamunce wa duk wanda ya karya wannan doka ba.
Bayan haka ya ce gwamnati za ta hada hannu da hukumar wayar da kan jama’a na Najeriya da hukumar kwallon kafa ta kasa, kungiyoyin matasa, da na mawaka domin tallata wannan shiri na gwamnati da bayyana irin illar da ke tattare da shan wadannan kwayoyi.
A jihar Katsina kwanakin baya Jami’an Hana Sha Da Fataucin Kwayoyi (NDLEA), sun kama wata zungureriyar tirela dankare da lodin maganin codeine maganin tari, har kwalba 24,0000, wanda matasa suka maida kwayar da su ke sha suna buguwa.
An kama babbar motar ne a Katsina, kamar yadda Babbar Kwamandar NDLEA ta Katsina, Maryam Sani ta bayyana wa manema labarai yau Talata a Katsina.
Ta kara da cewa an kama mutane shida masu alaka da safarar maganin daga Anacha.
Ta ce an kama direban motar, wani mai taimaka wa direban ya na tukawa idan ya gaji, da kuma kwandastocin motar su biyu.
Maryam ta ci gaba da cewa sauran wadanda aka kama su ne manajan kamfanin Sunglow Equity Nig. Ltd, wanda ake zargin shi ne mai maganin, da kuma jami’in da ke sayar da kaya a kamfanin.