Maka El-Zakzaky da gwamnatin Kaduna ta yi kotu, abin takaici ne – Kungiya

0

Wata kungiya mai rajin kare wadanda aka zalunta a ko’ina, mai suna Access to Justice, ta yi tir da Gwamnatin Jihar Kaduna a bisa maka shugaban mabiya Shi’a na Najeriya kotu.

Gwamnatin Kaduna ta kai karar sa ne inda aka zarge shi da laifuka guda takwas, ciki har da laifin kisa da aka ce ya afku a cikin watan Disamba, 2015, ranar da mabiyan sa suka yi hargitsi da sojoji a Zaria.

A hargitsin dai sojoji sun kashe mabiyan sa 348, yayin da soja daya ya rasa ran sa.

Fadan ya afku ne bayan da mabiyan malamin suka tare hanya, suka hana tawagar Shugaban Hafsoshin Sojan Kasar nan, Tukur Buratai wucewa.

“Irin yadda gwamnatin jihar Kaduna ta nuna rashin kunya da rashin sanin ya kamata, har ta ke neman hakkin soja daya da ya rasa ran sa, alhali ta kau da kai ga al’umma sama da 348, ta nuna rayukan su da ta kashe ba a bakin komai suke ba, hakan rashin tausayi ne, wulakanci ne, zunubi ne kuma bai yi daidai da kowace irin tafarkin dimokradiyya ba.”

Haka Daraktan kungiyar mai suna Joseph Otteh ya bayyana a Lagos.

Ya ce shi bai ma taba ganin nuna bambanci, bangaranci da tozarta rayukan al’umma irin na wannan mataki da gwamnatin jihar Kaduna ta aikata ba.

Ya ci gaba da cewa abin fa abin firgitarwa ne kuma abin kyama.

“Wato gwamnatin mu a yanzu sai wanda ta ga dama ta fifita, shi ne za ta kare masa ‘yancin sa. Sauran da babu ruwan ta da su kuma, ko oho!”

Sauran wadanda aka maka kotu tare da El-Zakzaky sun hada da matar sa Zeenat, Yakubu Katsina da Sanusi Kokori.

Wasu caje-cajen da ake yi musu ya hada da: Tare hanya, amfani da muggan makamai da kuma kafa shinge kan hanya suka hana tawagar Buratai wucewa.

Share.

game da Author