Wata kungiya ta nemi ‘yan majalisa su dawo da kudaden aringizo

0

Kungiyar rajin kare hakkin jama’a mai suna SERAP, ta yi kira ga ‘yan majalisar dattawa da ta tarayya da su maida kudaden alawus-lawus da suke karba baya ga albashin su.

A cikin wata takarda da mataimakin daraktan su Timothy Adewale ya sa wa hannu, sun yi kira ga Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Bukola Saraki da Kakakin Majalisar Tarayya Yakubu Dogara, su jawo hankalin sauran mambobin baki daya, su maida kudaden da aka rika yi musu aringizo, tunda ba da gumin goshin su suka samu kudaden ba.

Sun yi wannan kira ne yayin da a jiya Hukumar Raba Kudade da Kayyade Albashin Ma’aikata ta Kasa, ta bayyana ainihin albashin da alawus din da ‘yan majalisar ya kamata su rika karba, ta na mai cewa duk wani karin aringizon da ya wuce haka, to haramtacce ne.

Hukumar ta ce ita dai a karan kanta ba ta rattaba wa kowane dan majalisar dattawa karbar naira milyan I3.5 a kowane wata ba.

Sannan kuma ta ce ba da iznin ta ake biyan kowane dan majalisar tarayya naira milyan 10 a kowane wata ba.

Kungiyar SERAP ta ce tunda dai an fallasa cewa majalisar ce da kan ta suka yi wa junan su wannan kari na aringizo, kuma ga shi an tabbatar da cewa haramtacce ne, to ba za a yafe musu ba, sai sun dawo da ko nawa ne kowanen su ya karba a iyar tsawon shekarun da ya kwashe ya na wakilci a majalisar.

Share.

game da Author