An daure malamin da ya yi wa ‘yar shekara bakwai fyade

0

dunar ‘yan sandan jihar Filato ta gurfanar da wani malamin makaranta mai suna Moses Danladi dan shekara 23 a kotun Kasuwan Mama dake karamar hukumar Bassa kan yi wa ‘yan shekara bakwai fiyade.

Dan sandan da ya shigar da karan E.A Inegbonoise ya bayyana wa kotun cewa Danladi wanda ke zama a ‘Kisaghyip Federal Low Cost’ ya aikata haka ranar 15 ga watan Maris.

Ya ce sun sami labarin laifin da Danladi ya aikata ne bayan karar da kawun yarinyar mai suna Zakka Peter ya kawo caji ofis.

Zakka ya bayyana mana cewa yariyar ce ta fada masa cewa malamin na ta ya danneta ne da karfin tsiya a makaranta.

Bayan haka alkalin kotun H. Lawal ya yanke wa Danladi hukuncin zama a kurkuku har sai an gama shari’ar da aka daga zuwa ranar 9 ga watan Mayu.

Share.

game da Author