Rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa ta sanar da mutuwar wata yarinya mai suna Gambo Jibrin ‘yar shekara 17 a karamar hukumar Birnin Kudu.
Kakakin rundunar Abdu Jinjiri ya sanar da haka da yake zantawa da kamfanin dillancin labaran Najeriya ranar Litini a Dutse inda ya ce Gambo ta kashe kanta ne bayan ta kwankwadi maganin bera ‘Fiya-Fiya’.
Jinjiri ya ce sun mika gawan Gambo ga iyayen ta don yi mata sutura sannan za a gudanar da bincike gano musabbabin aikata hakan da ta yi.