Gwamnatin tarayya ta yi wa gamayyar kungiyoyin ma’aikatan jinya ‘JOHESU’ barazanar dakatar da albashin su idan har basu janye yajin aikin da suka fara ba.
Ta ce idan har basu dakatar da wannan yajin aiki ba za ta kafa dokar (Duk wanda bai yi aiki ba, ba Albashi).
Darektan yada labaran ma’aikatar Kwadago Samuel Olowookere ne ya shaida wa masu yajin aikin.
Olowookere ya bayyana cewa gwamanti ta dauki wannan mataki ne gani cewa ta biya duk bukatun kungiyar da ya hada da biyan albashin ma’aikatan da aka yi wa karin girma, karin albashi da sauransu bisa ga yerjejeniyar da suka yi a ranar 30 ga watan Satumba.
” Yajin aikin da kungiyar JOHESU ta shiga ya matukar ba mu mamaki duk da kokarin da gwamanti ke yi don biyan bukatun kungiyar’’.
Olowookere ya ce a dalilin haka gwamnati ta yi kira da kungiyar JOHESU da ta janye wannan yajin aiki domin ceto rayukan marasa lafiya a asibitocin kasar nan ko kuma ta fara aiki da wannan doka na kin biyan duk wanda bai zo aiki ba.
Bayan haka mataimakin shugaban kungiyar na kasa Ogbonna Chimela ya karyata biyan duk bukatun su da gwamanti ke ikiran ta yi.
” Bisa ga yarjejeniyar da muka yi da gwamnati kamata ya yi ta yi amfani da sabon tsarin biyan albashi na COMESS ne amma har yanzu shuru ka ke ji, bata ce komai ba.
Ya ce barazanar gwamnati ba zai ba kungiyar tsoro ba, ta na nan a kan bakan ta.
” Ba yau muka fara jin irin wannan barazana daga gwamnati ba sannan wannan dokar da suke babatun kafawa ba za ta yi tasiri ba.”
SHIN KO YAJIN AIKIN JOHESU YA YI TASIRI?
PREMIUM TIMES ta kai ziyara wasu asibitoci dake babban birnin tarayya Abuja domin ganin ko wannan yajin aiki yayi tasiri ko A’A?
Da muka je asibitin tarayya dake Abuja, ‘National Hospital’ ya bayyana mana cewa lallai wannan yajin aiki na JOHESU yayui tasiri a asibitin domin kuwa ma’aikatan asibitin basu zo aik ba, sannan dalilin haka yasa marasa lafiya duk sun canza asibiti.
A asibitin unguwar Wuse kuwa, ma’aikatan jinya basu bi sahun ‘yan uwansu ba, domin munga kowa na aiki kamar yadda ya saba.
A karshe shugaban kungiyar JOHESU na kasa Josiah Biobelemoye ya yi kira ga ma’aikatan asibiti da su yi amfani da wannan lokaci na yajin aikin su wayar da kan mutane game da dalilan da ya sa suka shiga wannan yajin aiki.
Ya kumakara da cewa ma’aikatan jinya dake aiki a asibitoci na jihohin kasar nan da kananan hukumomi za su bi sahun su nan da makonni biyu idan har gwamnati bata biya bukatun su ba.