Hasalallun sojoji sun banka wa wani gari wuta a Benuwai

0

Wasu da ake zargi sojojin Najeriya ne sun yi ganin Naka dirar mikiya, inda suka banka masa wuta. Haka PREMIUM Times ta samu labari.

Sojojin sun kutsa cikin garin mai suna Naka, hedikwatar karamar hukumar Gwer ta Yamma cikin Jihar Benuwai da misalin karfe 11 na rana, kuma nan take suka fara banka wa gidaje wuta. Haka Shugaban Karamar Hukumar, Solomon Ayagah ya shaida wa Premium Times ta wayar tarho a yau Alhamis da rana.

Sai dai kuma har kusan karfe uku na yammacin yau, hatta shi kan sa Ayagah bai iya tantance ko mutane nawa ne aka rasa ko suka jikkata ba.

Amma Shugaban Karamar Hukumar ya tabbatar da cewa sojojin sun je daukar fansa ne bayan matasan garin sun kashe soja daya a ranar Laraba.

“An kashe wani soja ne, wanda kuma wasu batagari ne suka kashe shi. Na je na samu Brigade Kwamandan su a ranar da misalin karfe 4:30 na asubahin yau.

“Ya ba ni sunayen wadanda ake zargi, kuma mun damka musu biyar daga cikin su a lokacin. To a lokacin da muke kokarin mu kai su ne sojojin suka yi wa garin dirar mikiya, suka fara banka wa gidaje wuta.”

“Sun banka wa gaba dayan wani sashe na garin wuta, kuma yanzu haka mu na kira da a kai mana dauki ne, kuma mu na rokon sojojin su sassauata mana.” Inji Ayagah.

An ce sojojin sun shafe awa biyu su na banka wa garin wuta kafin su fice.

Naka gari ne da ke kimanin kilomita 45 daga Makurdi. Ayagah ya ce akasari duk gidajen wadanda ba su ji ba, ba su gani ba abin ya shafa, ba gidajen wadanda suka kashe sojan ba.

Share.

game da Author