Fadar Shugaban Kasa ta yi magana dangane da yadda ake caccakar Shugaba Muhammadu Buhari tun bayan abin da ake kallo kasassaba ce ya yi, inda ya furta cewa matasan Najeriya sangartattun ragaye ne kuma jahilai.
Da ya ke jawabi a cikin wata takarda da ya fitar a yau Alhamis, kakakin yada labaran Buhari, Femi Adesina, ya bayyana cewa an sauya kuma an lankwasa ma’anar abin da Buhari ke nufi.
Adesina ya ce masu mummunar manufa ne suka yi wa furucin na Buhari mummunar fahimta har ake ta cancana maganar a duk fadin kasar nan.
Adesina ya kara da cewa Buhari bai yi jam’u ba, kuma bai yi wa matasa kudin-goro ba, cewa ya yi “masu yawa a cikin su” bai ce “dukkan su” ba.
Ya ce kowa ya san Shugaba Buhari mutum ne mai kishin matasa kuma mai kaunar ganin ci gaban su, don haka babu yadda za a yi ya fito fili ya aibata su.
Daga nan sai ya yi nuni da irin yadda Buhari ke tutiya da dimbin matasan kasar nan da suka yi zarra a fannonin rayuwa daban-daban.