Fadar Shugaban kasa ta maida wa Obasanjo martani

0

Mai ba shugaban kasa shawara Kan harkar yada labarai, Femi Adesina ya bayyana cewa gwamnati ba za ta ce komai Kan abubuwan da tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya fadi game da gwamnatin Buhari ba.

A jiya ne Obasanjo ya yi fatafata da salon mulkin jam’iyyar APC da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari cewa sun gaza.

Obasanjo ya fadi haka ne da yake karbar bakuncin wata kungiya Mai suna ‘Sabuwar Najeriya 2019’, a Jihar Ogun.

Da ya ke amsa tambayoyi kan wannan korafi na Obasanjo a hira da ya yi da gidan Talabijin din Channels, Femi ya ce gwamnati ta riga da ta bayyana matsayin ta game da Kalaman Obasanjo tun a wancan lokaci da ya rubuta wa Buhari wasika.

” Bayan haka ba za mu daina fadin irin yadda gwamnatocin baya suka yagalgala Najeriya ba da kuma irin nasarorin da wannan gwamnati ta samu.

Ya ce Najeriya zata Iya bugun kirji ta ce ta Tara Kudi masu yawa a Asusun ta na kasashen waje.

Share.

game da Author