Talban Minna zai maka gwamnatin tarayya a kotu

0

Tsohon Gwamnan Jihar Neja, Babangida Aliyu, ya musanta cewa ya wawuri kudin gwamnatin tarayya a cikin shekaru takwas da yayi nan a mulkin jihar.

Aliyu, wanda shi ne Talban Minna, ya yi barazanar maka gwamnatin tarayya kotu domin a kawo masa hujjar da ta sa aka lissafa sunan sa a cikin barayin da suka saci kudin kasar nan.

Ya yi wannan barazanar ce a jiya Litinin kuma ya sa wa takardar hannu da kan sa.

“Ni ban san dalilin da ya sa gwamnatin tarayya ta tsarma suna na a cikin wadanda ta kira mutane 24 da su ka wawuri dukiyar jama’a ba. Ban san abin da ya sa Ministan Yada Labarai, Lai Mohammed ya saka suna na ba.”

Ya ce zai tattauna da lauyoyin sa, domin su gaggauta gurfanar da gwamnatin tarayya a kotu.

Ya ce karya ake yi masa, babu wani wanda ya tunkare shi har ya nuna masa wata takardar shaida wai ya karbi kudi har naira biliyan 1.6 a hannun Sambo Dasuki.

Ya ce sharri ne kawai da bata suna na gwamnatin APC.

Share.

game da Author