Ba zan yi takarar shugabancin Najeriya a 2019 ba, Inji Saraki

0

Jiya Litinin ne Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki ya musanta rahotannin da suka danganta shi da cewa zai tsaya takarar shugaban kasa a zaben 2019.

Saraki ya kara jaddada cewa rahotannin da aka danganta shi da zaben 2019, ba gaskiya ba ne, karya ce kawai.

A cikin wata hira da ya yi a jaridar Independennt, kakakin yada labaran sa, Yusuf Olaniyonu, ya ce kwata-kwata a cikin rahotannin babu kamshin gaskiya.

Wata mujalla mai suna Boss da Dele Momodu ke bugawa, ta ruwaito cewa Saraki zai tsaya takarar shugaban kasa a zabe 2019.

Olaniyonu ya kara da cewa da gaskiya ne labarin tsayawa takarar ai da an gani a sauran manyan kafafen nyada labaran kasar nan.

Share.

game da Author