El-Rufai zai sha ruwan kuri’u a 2019 fiye da yadda ya samu a 2015

0

Wasu daga cikin mazauna garin Kaduna da Kananan hukumomin jihar sun bayyana cewa tabbas idan har zabe ce zata dora mutum a kujerar mulki, gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai zai sha ruwan kuri’u a 2019.

Umar Muhammed, wani matashin dan siyasa ne da ke zama a garin Kaduna sannan mai bibiya da yin fashin baki ne a harkar siyasar Najeriya.

A hira da yayi da PREMIUM TIMES HAUSA Umar ya fide mana biri daga kai har wutsiya inda ya tabbatar mana cewa ” adawa ce kawai yake neman ya sumar da wasu a jihar Kaduna amma ko tantama bani da shi cewa El-Rufai zai yi raga-raga da duk wani da ya ce zai tsaya takara da shi.”

” Tsakani da Allah Idan ba hassada ba me nene kake so mutumin da kazaba yayi maka? Na san kowa zai ce aiki ko, toh a gaya min wani gwamna ne a ka taba yi a Kaduna kuma ya taba kwatanta abin da El-Rufai yake yi cikin kasa da shekaru uku da zabar sa?

” Gaskiyar magana ba a taba haka ba, ko gwamna Makarfi da ake cewa yayi aiki ai jumlar ayyukan da yayi ne a shekaru 8. El-Rufai ko ko shekara 3 bai cika ba tukunna amma aiki akeyi a ko ina.

Umar yayi kira ga mutanen jihar da su duba abinda akeyi a Jihar, babu birni ba kauye ko ina ne an budo aiki.

” Mu dai zamu ci gaba da gaya wa mutane gaskiya, su yi fatali da siyasa su koma su yi nazarin ta natsu.

Ita ko Sim John, yar asalin karamar hukumar Jaba ta bayyana mana cewa ne ko a karamar hukumar su can, suna ganin ayyukan ci gaba.

” Maganar aiki kam babu kamar gwamna El-Rufai, mun shaida kuma ko ina ne Ka zagaya za kaga wani abu da ake yi wa mutanen jihar Kaduna.

Mutane da dama da suka zanta da PREMIUM TIMES HAUSA sun nuna soyayyar su matuka ga irin ayyukan da gwamnatin Jihar take yi wa mutanen jihar.

Sai dai kuma wani hanzari ba gudu ba, duk da irin wannan yabo da gwamna El-Rufai ya sha wasu na ganin sam bai yi abin da ya kamata yayi ba wa mutanen jihar.

” Mu fa ba kwalbati da titi za mu ci ba, ya kora mutane aiki, sannan har yanzu ba ace musu komai ba. Kwalta za su kada su sha.” Inji wani mazaunin garin Zariya.

Share.

game da Author