Babu shakka, babu tantama, babu jikara kuma babu takoke, a yau idan aka ce a lissafa fitattu kuma kwararrun ‘yan wasan kwallon kafa a duniya, babu yadda za a yi a kira ‘yan wasa hudu zuwa biyar ba tare da an kira yaron nan matashi, dan kasar Masar, mai shekaru 26 kacal da haihuwa ba, wato Mohammed Salah.
Salah, wanda ya fara buga wa kungiyar Liverpool a wannan kakar wasa, ya samu daukaka a cikin shekara daya, wadda ‘yan wasa da dama suka shafe shekara da shekaru su na gaganiyar nema, amma ba su samu ba,
Nasarorin da ya samu cikin dan kankanen lokaci a wasan gasar Premier League na Ingila, ta jawo masa farin jini, har a a cikin kasashen duniya baki daya.
A yau da an ce Ronaldo, aka ce Messi, ko kuma aka ce Messi aka ambaci Ronaldo, to kafin a kira sunan wani dan wasa, Mohammed Salah za a kira.
Irin yadda magoya bayan kungiyar Liverpool ta Ingila su ke nuna masa so da kauna, an ce sun dade ba su nuna wa wani dan wasa shaukin so kamar yadda su ke muna wa Salah ba.
Duk yadda za ka kwatanta al’amarin Salah, to ya wuce nan. Yaro ne matashi, wanda ga dukkan alamu guguwar bushashar rayuwa ba ta debe shi ta yi awon gaba da shi ba.
Kasancewar sa Musulmin kasar Masar, zuwan sa Turai bai sa ya fizge da igiyar rikon addinin sa na musulunci ba. Ba ya shan barasa, ba ya neman mata, ba ya shan kwayoyi, amma akwai shi da rikon addini.
A duk Juma’a, Sallar Juma’a ba ta wuce shi. Haka salloli biyar su ma ya na yin su kan lokaci.
Irin yadda kafin a fara wasa ya ke bude hannaye biyu ya roki Allah sa’a, ya na burge masu kallo Turawa magoya bayan sa da goyon bayan kungiyar sa.
Bahaushe ya ce ‘bukatar ma-je-Hajji, sallah. Sai aka yi gamo-da-katar cewa kwallo a ke so Salah ya rika ci, kuma ita ya ke ci. To ai dalili kenan ake nuna masa kauna har ta ke neman ta wuce misali.
Da yawa sun a kiran sa da lakanin a-ci-kullum. Kananan yara Turawa masu kallon kwallo a talbijin kuwa, idan Salah ya ci kwalo su ma har irin sujadar nan su ke yi, irin wadda Salah ke yi.
Bari ma ku ji wata waka da ‘yan kallon kwallo ke masa a cikin sitadiyan idan wasa ya yi zafi:
“Mo Salah Salah la la la la,
Kai na mu ne,
Mu ma na ka ne,
Duk inda ka yi mu na biye da kai,
Ba za ka bar mu ba,
Ba za mu bar ka ba ba ba ba,
Idan ka ci min kwallo ko’ina ka shiga ga ga ga ga,
Sai na bi ka babu bata lokaci,
Ko Masallaci ka shiga ni ma zan shiga,
Ko Sallah ka ke yi ni ma za ni yi.”
A wannan kakar wasanni ta 2017/2018, Salah ya ci kwallaye 43. Wannan kuwa ba karamin tarihi ba ne ya ajiye. Domin dai babu wani dan Afrika da ya taba cin kwallye da yawa a gasar wasanni a Ingila kamar sa.
A wannan shekara kuma babu wani dan wasa a Ingila da ya kai shi cin kwallaye. Tuni ma har an ba shi kyautar Gwarzon Dan Wasan Firimiya na 2017/2018.
Saura kwallaye 4 kacal ya kamo Ian Rush, wanda a tarihi shi ne ya taba cin kwallaye da yawa har 47 a shekarar gasa daya a kungiyar Liverpool.
Idan muka koma kasar Masar, ko mu ce Egypt, Salah ya fitar da su kunya kuma ya share wa kasar hawayen kukan rashin zuwa gasar cin kofin duniya. Rabon da Egypt ta shiga gasar cin kofin duniya an haura shekaru 24, sai a wannan shekarar, albarkacin Mohammed Salah.
Irin yadda ake girmama shi a Turai, haka ake girmama shi a kasar sa. Domin ta kai a zaben shugaban kasa da aka gudanar a kasar cikin watan Mayu, ya samu kuri’u sama da miliyan daya, duk kuwa da cewa shi ba ya daga cikin ‘yan takara.
Da yawan masu kada kuri’a sai su rubuta sunan ‘Mohammed Salah’ a matsayin wanda su ke so ya zama shugaban kasar Masar.
Mu koma kasashen Turai, inda can ne dandali da majalisar taka leda a duniya.
Mohammed Salah shi ke bi wa Christiano Ronaldo a yawan kwallaye a gasar Zakarun Turai. Ronaldo na da kwallaye 15, Salah na da 10. Albarkacin Salah, Liverpool ta kai wasan kusa da na karshe. Ta ci Roma ta kasar Italy kwallaye 5. Har sai lokacin da mai horas da kungiyar Liverpool ya cire Salah daga wasan, sannan Roma ta samu jefa kwallaye biyu kawai.
Duk sanaben da Messi ke yi, Salah ya iya. Duk sanaben da Ronaldo ke yi, Salah ya iya. Takamar Messi da Ronaldo yin shiga a haka a cikin yadi 18 a jefa kwallo a raga. Shi ma Salah ya iya.
Yadda kowace kungiya ke tsoron karo da Ronaldo ko Messi, a yau haka kowace ke tsoron karo da Mohammed Salah.
UKU DUWATSUN MURHU
Kamar yadda Barcelona ta ke takama da Messi da Suarez da Neymar a wancan lokacin, kamar yadda Real Madrid ke takama da Ronaldo da Benzema da Bale, to haka Liverpool ke takama da Salah, Sadio Mane da Roberto Firmino.
Su Salah su uku a bana sun ci kwallye 92, su Ronaldo kuwa 90, su Messi 86. Idan haka ne kuwa, Bahaushe ya yi gaskiya da ya ce ‘Na kawo karfi ya fi wane ya girme ne.’
Sai dai me, magana ta gaskiya sai an kai nan da shekara takwas kafin a fara kwatanta Salah da Messi da Ronaldo. Su yanzu su ke kai gangara. Shi kuwa yanzu ya ke kan ganiya.
Wannan kuwa mu ta shafa, babu ruwan Liverpool. Domin a yau duk inda Liverpool ta shiga, ta na bugun kirjin cewa, ‘ina gwanin wani, ga nawa?’
Da zan yi ido da ido da Salah, ni ba waka zan yi masa ba. Sai dai na kalle shi, saboda mamaki da al’ajabi, na ce masa, ‘Zurke dan Muhamman!’ Shi kuma na san dariya zai yi, ya buga kafa kasa, ya ce min, ‘Himma dai dan Shehu!’
Discussion about this post