Shugaban hukumar kula da cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko na jihar Bauchi (BSPHCDA) Ibrahim Gamawa ya tabbatar da cewa mutane uku sun rasu daga cikin mutane 25 din da ake zaton sun kamu da cutar zazzabin Lassa a kananan hukumomi 7 dake jihar.
Ya ce wadannan kananan hukumomin sun hada da Alkaleri, Bauchi, Bogoro, Dass, Tafawa Balewa, Toro da Warji.
Gamawa ya sanar da haka ne a taron wayar da kan jama’a game da illolin dake tattare da cutar wanda aka fara ranar Talata a Bauchi.
Ya kuma kara da cewa tsakanin watannin Janairu zuwa Maris sun sami tabbacin mutane biyar da suka kamu da cutar daga cikin 25 din da ake zaton sun kamu da cutar.
Gamawa ya yi kira ga ma’aikatan kiwon lafiya da su tabbata sun yi wa duk wanda ke fama da zazzabi ko wani irine gwaji kafin su bashi magani.
” Ya kuma kamata ma’aikatan kiwon lafiya da mutanen dake jinyar ‘yan uwansu da suka kamu da cutar su yi hattara da kan su kada garin neman kiba a samo rama.”
Sannan ya yi kira ga mutane da su tabbata suna tsaftace jikin su, muhallinsu da abincin su domin hakan ne hanyar samun kariya daga kamuwa daga cutar.